Ticker

6/recent/ticker-posts

7.3 Daudun Bara - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 143)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

7.3 Daudun Bara 

Wannan waƙa ma yara ne suka fi gudanar da ita, musamman almajirai. Ga yadda waƙar take:

Ni Daudun bara ɗan Galadiman bara,

Na saba bara ba na kwana ban ci ba,

Kun ga rawar tuwo kun ga tattaken miya,

Kun dafa kudaku abin cika mummuƙe,

Kak ka ci kak ka sha rabon wani ba naka ba.

Idan naka ne kana ɗaka aka ba ka shi.

Kura ta ga ɗan bara ɗan almajiri,

Bari in bi ka ɗan bara in shawo gari.

Tahiya da taki ba ta zama ɗai da ɗai,

Ni roƙo ni kai ga mata ‘yan arziki,

Ke ƙwace ki kai ga mata ba su ba ki ba.

Mai babban rabo ba zai wuce aljanna ba.

Su ɗebo da kaɗan-kaɗan su ba dai almajiri.

Inna in ba ki ba ni ba inai maki kukan gada:

Innaaaaahhhh!

Inna in ba ki ba ni ba zan yi na saniya,

Innaaaahhh!

Inna in ba ki ba ni ba zan yi na tunkiya,

Innaaaah!

Inna in ba ki ba ni ba, ni zan kwan a nan.

Wannan waƙa tana ɗauke da barkwanci da ban dariya, musamman yayin da aka ga Daudun bara na kwatanta rawar tuwo ko kuma tattaken miya. Wannan salo kaɗai ya isa jan hankalin wanda ake roƙa domin ya ba da sadaka. A cikin waƙar an kawo alamci inda ake kwatanta ɓarayi da kura. Mai waƙar na nuna shi ba sata yake yi ba, yana roƙa ne a ba shi. Ɓarayi kuwa na ɗauka ne ba tare da an ba su ba. Daga ƙarshen waƙar kuwa ya kawo barkwanci, inda yake kiran inna, cikin yanayin kukan dabbobi daban-daban. Daga ƙarshe ma ya nuna cewa, ba zai tafi ba har sai inna ta ba shi sadaka, idan ba haka ba kuma to zai kwana a wurin (lallai kuwa gwara inna ta rufa wa kanta asiri ta sallami ɗan almajiri).

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments