Ticker

6/recent/ticker-posts

7.2 Saboda Manzon Allah - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 141)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

7.2 Saboda Manzon Allah

Wannan ta kasance ɗaya daga cikin waƙar bara da mabarata ke amfani da ita a ƙasar Hausa. Ba mutum guda ke rera wannan waƙa ba, a maimakon haka, akan samu mabarata musamman daga uku zuwa sama. Ɗaya daga ciki zai riƙa bayarwa, saura kuwa za su riƙa amsawa. Sannan manya ne aka fi saninsu da wannan waƙa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Masu gida salamu alaikum,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: Ku ba mu domin Allah,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: Domin Manzon Allah,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: Alhaji ko Modibbo,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: Ko Hajiya mai niyya,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: A ba mu domin Allah,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: Domin Manzon Allah,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: Ita sadaka guzuri ce,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: A ba mu don Lillahi,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: A ba mu don mai janna,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

 

Bayarwa: Ga wanda Allah Yab ba,

Amshi: Saboda Manzon Allah.

Haƙiƙa wannan waƙar bara tana ɗauke da jigon roƙo ne kai tsaye, inda masu barar ke haɗa wanda suke roƙo da Allah da kuma Manzonsa domin a ba su sadaka. Daga ciki kuma sun yi furucin girmamawa ga wanda suke roƙa, wato inda suke faɗin Alhaji da Modibbo da kuma Hajiya. Bayan nan sun yi jan hankali kan cewa sadaka guzuri ce, ke nan dai duk wanda ya ba su zai samu sakamakon alkairi, musamman ranar gobe kiyama.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments