Ticker

6/recent/ticker-posts

5.7.8 Waƙar Tatsuniyar Cin Amanar Ɗan Uwa - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 128)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

5.7.8 Waƙar Tatsuniyar Cin Amanar Ɗan Uwa

Ƙashi: Kai bokan nan nan,

 Ƙashina ne kake hurawa,

 Baba ya aike mu daji,

 Mu samo furannin ƙawa,

 Nawa sun fi na ɗan uwana kyau,

 Sai ya ƙwace nawan,

 Ya kashe ni.

 

Ƙashi: Kai sarkin nan,

 Kai sarkin nan,

 Ƙashina ne kake hurawa,

 Baba ya aike mu daji,

 Mu samo furannin, ni da yayana,

 Nawa sun fi na wana kyau,

 Sai ya ƙwace nawan,

 Ya kashe ni.

 

Ƙashi: Kai Babana, kai Babana,

 Ƙashina ne kake hurawa,

 Kai ka aike mu daji,

 Ni da wana, mu samo furanni,

 Nawa sun fi nasa kyau,

 Sai ya ɗauke nawan,

 Ya kashe ni.

 

Ƙashi: Kai yayana, kai yayana,

 Ƙashina ne kake hurawa,

 Baba ya aike mu daji,

 Mu samo furanni,

 Nawa sun fi naka kyau,

 Sai ka ɗauke nawan,

 Ka kashe ni.

 (Usman, 20094: 24)

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments