Ticker

6/recent/ticker-posts

5.7.5 Waƙar Tatsuniyar Daskindariɗi - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 127)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

5.7.5 Waƙar Tatsuniyar Daskindariɗi 

Daddawa: Assalam salam ɗan yaro assalam salam,

Ɗan Yaro: Wace ce nan take mini assalam salam?

 

Daddawa: Daddawarka ce take maka assalam salam,

 Mai sa miya daɗi ɗan yaro,

 Mai sa miya daɗi.

Ɗan Yaro: Na ji naki suna yarinya faɗi nawa suna.

 

Daddawa: Daskindariɗi ɗan yaro Daskindariɗi,

Ɗan Yaro: Buɗe ki shigo yarinya, buɗe ki shigo ki sha daɗi.

(Yakasai, 2012: 18).

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments