Ticker

6/recent/ticker-posts

4.9.1 Rerawa A Kaɗaice

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.9.1 Rerawa A Kaɗaice

Mabarata manya da yara maza ko mata sukan tafi yawon bara suna yin waƙa, su kaɗai ba tare da wani mai amshi ba. Za su riƙa bi waje-waje suna rera waƙar suna bara da ita. Misali:

 Kwalho uwata kwalho,

 Kwalho ma almajiri,

 Almajiri nike ɗan malami,

 Nike mai tukkuwar shan gumba

 (Kwalho)

Wanna waƙar almajirai ke yin ta. Kuma mutum ɗaya ne ke rerawa yana yawo rariya-rariya domin bara ga jama’a ba tare da wani mai yi masa amshi ba.

 1. Na roƙi Jallah abin nema na,

Don wanda kai cikakken suna,

Ka kai ni Makka abin fatana,

 In zama Alhaji can wata rana.

 2. Mun gode Jallah Ta’ala Sarki,

Sa mu ga Annabi ko a mafarki,

Duk wanda bai iya wankan tsarki,

 Ƙarshensa ai masa suna jaki.

 3. Ina gaya maku ‘yan makaranta,

Da ku samari da ku ‘yan mata,

In an gaya mana a ba ca ta,

 Sai mu riƙe su mu zam ‘yan gata.

 4. Rashin sani ga mutum ƙauyanci,

 Nemi sanin ilmi binnanci,

 Kai ƙoƙari ka yi komai ɗaci

 Ko a Kano kake ko kuma Bauchi.

 5. Almajiri nake ba ni da komi,

 Mai shan fura nake ko tai tsami,

 Gun Jallah zan biɗi sauƙin komi,

Ba gum mutum ba da ba shi da komi

 (Adamu Jingau Furfuri:Waƙar Gargaɗi)

Wannan waƙar rubutacciya ce wadda mabarata kan zagaya a yankin ƙasar Hausa suna rera ta a kaɗaice ba tare da wani mai yin amshi ba. Duk lokacin da aka ji mabaratan suna tafiya suna rangaɗa wannan waƙar sai a riƙa miƙa masu sadaka ko ma a aiko da sadakar daga cikin gida ko wani wuri da suka riga suka wuce.


Post a Comment

0 Comments