Ticker

6/recent/ticker-posts

4.5.1.1.1 Waƙar “Daudun bara”:

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

 4.5.1.1.1 Waƙar “Daudun bara”:

Jagora : Ni daudun[1] bara,

: Ɗan Galadiman bara.

 Amshi : To.

 Jagora : Na saba bara,

: Ba ni kwana ban ci ba.

 Amshi : To.

Jagora : Kun ga rawat tuwo,

: Kun ga sassakad[2] dawo,

: Kun ga kalmaɗaren miya.

 Amshi : To.

 Jagora : Ko kun dahwa kudaku,

: Abincin cika mummuƙe

 Amshi : To.



[1]  Sunan Daudu yana nufin wani mutum mai gata, a wasu wurare kamar Anka ta jihar Zamfara idan an kira mutum Daudu to mutum ne wanda ya gaji sarauta.

[2]  Sassaka dai kamar gudu-gudu ne amma ba gudu ba, shi kuma ba tafiya ba - hanzari.

Post a Comment

0 Comments