Ticker

6/recent/ticker-posts

4.5.1 Waƙar Ɗan Gazari - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 117)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

4.5.1 Waƙar Ɗan Gazari 

A gargajiyance, bayan an ɗaura aure, al’ada ta tanadi abin da ake kira ‘wankin ango’. Bayan an kammala wannan taro na wankin ango, akan raka shi zuwa gidajen manyan ‘yan uwan amarya domin gaisuwa da godiya, tare kuma da yi musu addu’ar alkairi da zaman lafiya dangane da auren da aka ɗaura. Bayan an kammala wannan ziyara, a hanyar dawowa gida (zuwa gidan ango) akan rera wannan waƙa ta ‘Ɗan Gazari’. Waƙar ta kasance kamar haka:

Bayarwa    Amshi

Ɗan gazari-gazari,   Yamma

Ango yana rawa,   Yamma

Aboki yana rawa,   Yamma

Arwanka na rawa,   Yamma

A gaishe ku da rawa,  Yamma

Ango da amarya,   Yamma

Ango na amarya,   Yamma

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments