Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
4.4 Waƙar Assalamu Alaikum
Wannan ma na ɗaya daga cikin waƙoƙin aure na ƙasar Hausa. Sai dai an fi rera wannan waƙa yayin da aka iso cikin gidan ango. Waƙar ta kasance kamar haka:
Bayarwa: Assalamu alaikum,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Masu gida ku buɗe ƙofa,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Masu gida ku buɗe ɗaki,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Ga ɗiyarmu nan mun kawo,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Mun kawo ta ɗakin ango,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Ɗiyarmu ba ta tsegumi,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Ɗiyarmu ba ta ƙarya,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Ango ga ɗiyarmu nan,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Kar ka je ka koya mata ƙarya,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Kar ka je ka koya mata tsegumi,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Muguwar sarkuwa ja’ira,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: A jefa mata bargon ‘yan wuta,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Haihuwa muke kira har kullum,
Amshi: Assalam!
Bayarwa: Haihuwa muke kira gun Allah.
Amshi: Assalam!
Haƙiƙa idan aka lura da wannan waƙa akwai saƙwanni masu muhimmanci da za a iya tsinta ciki. Masu rakiyar amarya dai sun yi wa ‘yan uwan ango sallama, tare da danƙa musu amanar ɗiyarsu. Sun kuma bayyana musu cewa, ɗiyarsu mutumiyar kirki ce, wanda ba ta ƙarya ko tsegumi. A dalilin haka suke jan kunnen ango da kada ya kuskura ya koya wa ɗiyarsu waɗannan munanan halaye. Daga nan kuma sai suka yi hannunka-mai-sanda zuwa ga tasirin ‘yan uwan miji wurin daidaitar aure ko rugujewarsa, wato musamman uwar miji (sarkuwa). Inda suka nuna cewa, sarkuwa mai mugun hali da ta-da-zaune-tsaye ba za ta yi kyakkyawar makoma ba. A ƙarshe kuwa, addu’a suka yi ga auren baki ɗaya, wato na a samu zuriyya. (haihuwa).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.