Ticker

6/recent/ticker-posts

4.3 Ayyaraye Daure Jure - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 113)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

4.3 Ayyaraye Daure Jure 

Wannan na ɗaya daga cikin waƙar da ta sanu sosai a ƙasar Hausa a ɓangaren bukin aure. Sai dai duk da cewa akan rera wannan waƙa yayin raka amarya, an fi rera ta lokacin da ake yi wa amarya ƙunshi (sakun lalle). A wannan lokaci ne mata, musamman ‘yan mata (abokan amarya) ke riƙa rera wanna waƙa. Ɗaya daga ciki za ta riƙa bayarwa yayin da saura ke amsawa, kamar haka:

Bayarwa: Ayyaraye daure jure,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: ‘Yar tsohuwa mai ɗan ƙoƙo,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Allah Ya kashe ki mu sha gumba,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: ‘Yar tsohuwa mai ɗan ƙoƙo,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Allah Ya kashe ki watan gobe.

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Yarinya daure-daure,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Ba a kanki ne aka fara ba,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Kuma ba a kanki ne za a ƙare ba,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Aure cikin farilla ne,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Da babu shi ke ma ba kya zo ba,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: A yau aurenki ake yi,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

 

Bayarwa: Gobe na ɗiyarki za ay yo,

Amshi: Ayyaraye daure jure.

Ga bisa dukkan alamu, tsohuwar da ake yi wa addu’ar mutuwa a nan ita ce wadda ke ƙunsa wa amarya lalle. A cikin waƙar ana ba wa amarya haƙurin rabuwa da za ta yi da ‘yan uwa da kuma killace ta da za a yi wuri ɗaya, ba tare da fita yawo kamar yadda ta saba ba kafin aure. Ana kuma nuna mata cewa, ba fa a kanta ne aka fara hakan ba, kuma ba a kanta ne za a ƙare ba. Daga ƙarshe ma sai ake nuna mata shi fa wannan aure dole ne, domin da ba don shi ba, ita ma kanta ba za ta zo duniya ba. Sannan a dalilinsa ne za a yi wa ɗiyarta aure watan wata rana.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments