Ticker

6/recent/ticker-posts

4.2 Ayyaraye - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 112)

 Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

4.2 Ayyaraye

Wannan ma waƙa ce da akan rera yayin da ake kan hanyar raka amarya ɗakin angonta. Ɗaya daga cikin masu rakiyar za ta riƙa bayarwa, saura kuwa suna amshi. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ayyaraye nanaye,

Amshi: Wa aka yaye?

 

Bayarwa: Sadiya,

Amshi: Wa za a kai wa?

 

Bayarwa: Amadu,

Amshi: Ayyuriri mu yi guɗa.

 

Bayarwa: An yaye, an yaye,

Amshi: Eh, an yaye.

 

Bayarwa: Shekaranjiya,

Amshi: Wa aka yaye?

 

Bayarwa: Sadiya,

Ko ba ta kai ba?

Amshi: Ayyuriri,

 Ta kai,

 Wa aka bai wa?

 

Bayarwa: Amadu,

 Ko ba ku bayar ba?

Amshi: Mun bayar.

 

Bayarwa: Mun ba shi har ga Allah,

Amshi: Mun bayar,

 Ayyaraye nanaye.

Haƙiƙa wannan waƙa tana bayyana sunan ma’aurata ga sauran jama’ar gari, musamman waɗanda ke kan hanyar da masu raka amarya ke wucewa. Wannan kuwa na faruwa ne kasancewar waƙar na bayyana sunan ma’auratan ƙarara.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments