Ticker

6/recent/ticker-posts

4.1 Ayye Mama - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 111)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

4.1 Ayye Mama 

Wannan ɗaya ne daga cikin waƙoƙin da akan rera yayin raka amarya ɗakinta. Yawan masu rera wannan waƙa ya danganta ga adadin ƙawayen amarya da sauran maƙarraban (mutane) da ke cikin zuw aga rakiyar amaryar. Yayin da aka ɗunguma zuwa gidan amarya, ɗaya daga cikin abokan amaryar za ta sanya waƙa. Saura kuwa za su riƙa amsawa tare da tafi. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ayye mama ayye mama,

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Ayye Halima kin tafiyarki?

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Don haka kin shige ɗakinki?

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: An ce Halima mun rabu ke nan?

Amshi: Mamaye iye.

 

Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

Amshi: Mamaye iye.

Haka za a ci gaba da yi har sai an isa ɗakin amarya ko kuma an canza wata waƙa daban.Wannan waƙa tana samar da nishaɗi ga masu raka amarya. Duk nisan wuri kafin a farga za a ga har an iso saboda shagaltuwa da aka yi da waƙe-waƙe. Bayan haka waƙar na ɗauke da saƙon bankwana zuwa ga amarya.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments