Ticker

6/recent/ticker-posts

3.5.4 Ƙazama - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 109)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.5.4 Ƙazama

Kamar dai yadda sunan waƙar ke nunawa (ƙazama), tana ɗauke da jan hankali zuwa ɗabi’ar tsafta. Ga yadda waƙar take:

Zanka wanka da wanki,

Ke yi maƙal-maƙal.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi daƙal-daƙal.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi ƙazan-ƙazan.

 

Zanka wanka da wnki,

Ke yi mujur-mujur.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi kuca-kuca.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi kurun-kurun.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi ƙirin-ƙirin.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi baƙi ƙirin.

 

A’a wanke zannanki sauna,

Sun yi tilin-tilin,

 

A’a zanka wanka da wanki,

Ko kya yi fari-fari. (Illo, 1980: 8)

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments