Ticker

6/recent/ticker-posts

3.2.1 Mu Je – Mu Je - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 100)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.2.1 Mu Je – Mu Je

Wannan na ɗaya daga cikin waƙoƙin daɓe. Tana ɗauke da kalaman azama ga masu aikin, tare da shaguɓe musamman ga masu wasu muggan halaye kamar su ƙarya ko zunɗe da makamantansu.

Bayarwa: Mu je – mu je.

Amshi: In mun je ba dawowa.

 

Bayarwa: Za a da ni,

Amshi: Ba za a da ke ba,

 Mai tsince,

 

 Ba za a da ke ba,

 Mai ƙarya.

 

 Ba za a da ke ba,

 Mai zunɗe.

 

Bayarwa: Mu je – mu je,

Amshi: Shan furanmu ikon Allah,

 In mun je ba mu dawowa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments