Ticker

6/recent/ticker-posts

3.5.3 Naƙuda Ta Tashi - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 108)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.5.3 Naƙuda Ta Tashi

Wannan waƙa na ɗaya daga cikin waƙoƙin da mata ke rerawa yayin niƙa. Ta kasance kamar haka:

 

Wayyo naƙuda ta tashi,

Ciwon naƙuda ya tashi.

 

Kuma ciwon naƙuda ya motsa,

Yau kam babu zama zaure.

 

Wayyo Inna ki cece ni,

Ciwon naƙuda ya tashi.

 

Da kis sha daɗinki,

Ke tuna da Inna ta cece ki?

Ko ke tuna da baba ya cece ki?

Wayyo naƙuda ‘yar ziza!

 

Ciwon naƙuda bori ne,

Ko ko naƙuda hauka ce!

 

Wayyo naƙuda ta tashi,

Wayyo naƙuda ta motsa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments