Ticker

6/recent/ticker-posts

3.5.2 Waƙar Kishiya - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 107)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.5.2 Waƙar Kishiya

Wannan ma na ɗaya daga cikin waƙoƙin niƙa da mata ke yi. Kai tsaye mai waƙar na takalar kishiya ne. Ga yadda waƙar take:

Ayye yaraye iye nanaye,

Ayye yaraye iye nanaye.

 

Ga wata kishiya ruwan sanyi  ce,

Wata ko na zafi ya fiye mata.

 

Kishi da ‘yar Malan nake gudu,

Ta yi maka magani ta saka a hanya.

 

Hanyar gidanku ta barbace maka,

Allah ba ni kishiya mai yaji.

Kamin ta dawo na ci duniya.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments