Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
3.5.1 Zakkar Gida
Wannan waƙa na ɗaya daga cikin waƙoƙin da mata ke rerawa yayin da suke niƙa. Waƙar ta kasance kamar haka:
Hannunta ba shi tashi ga daka,
Ga cin tuwo yaka tashi.
Tasa uku hitarta faɗuwarta,
Ɗauki mai laƙaƙƙe-laƙaƙƙe.
Mai laƙaƙƙen hannu,
Da ba shi tashi ga daka,
Ga cin tuwo yaka tashi.
Malmala taka loma da ita,
Gidauniya kurɓi ukku takai mata.
Ban kula ba, ban sa kai ba,
Ban kula ba da marin ƙato,
Balle na ɗan jariri.
Ɗauki-ɗauki in tanye ki,
In ba ki so in ɗebo.
Zama daka tanyo ne,
Ido ka tsoron aiki,
Hannu na faɗin a kawo mu gani.
Maccen kurku maccen banza,
Maccen da ba ta wa namiji isa.
(Illo, 1980:11)
Wannan waƙa na ɗauke da habaici, inda mai waƙar ke yi da wata cewa malalaciya ce (magandaciya); wanda ba ta da ƙoƙari wurin aiki amma sai cin abinci kamar gara. Kuma ta nuna cewa, duk abin da take yi (abokiyar takun saƙar mai waƙar), ko a bakin zanenta, ma’anar ba ta damu ba (tamkar yaro ne ya doke ta, alhali ko dukan babba ma bai ishe ta waige ba). A gaba kuma take nuna kuzari da ƙarfin guiwar da take da shi ga aikin da ke gabanta, inda take nuna ba ta tsoron aikin. A ƙarshen waƙar kuwa, sai ta sake komawa ga habaicin da take yi, inda take nuna abokiyar yin nata ba kowa ba ce ko a wurin miji.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.