Ticker

6/recent/ticker-posts

3.4.2 Ta Yi Kitsonta - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 105)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.4.2 Ta Yi Kitsonta

Wannan waƙa ma mai kitso ne ke rerawa yayin da take yi wa wata kitso. Makitsa sun fi rera wannan waƙa yayin da suke yi wa ƙananan yara kitso. Ga yadda waƙar take:

Ta yi kitsonta,

Beru tai saƙarta.

 

Ta sai ɗan zanen ɗaurawa,

Ta fita.

 

Wagga Agola,

Ta zo ta ɗauke shi.

 

Wagga Agola,

Ko kitso ba ta iyawa.

 

Wagga Agola,

Ai babu irinta,

 

Baƙar Agola,

Ta hana mata sauran zanensu.

 

Ke dai Beru,

Zanka kitsonki.

Idan aka lura da saƙon da waƙar ke ɗauke da shi, za a ga cewa Makitsiya kamar rarrashi ko lallaɓa take yi ga wadda take yi wa kitso. Makitsiyar na yabon Beru da cewa ta yi kitso tsaf-tsaf, kuma ba ta neman fitana, sai ma takalar ta da ake yi da faɗa. Kuma take ba ta shawara da ci gaba da zama lafiya tare da yin kwalliyarta (kitso) ta rabu da mai takalar ta faɗa (Agola).

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments