Ticker

6/recent/ticker-posts

3.4.1 Mai Kitso - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 104)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.4.1 Mai Kitso 

Wannan waƙa mai kitso ke rera ta yayin da take yi wa wata kitso. Ga yadda waƙar take.

 

Mai kitso ‘yar salama.

 

Ka da mata ki taushe.

 

Ke ka da mata ki kalmoshe.

 

Ko da gidan mai gari ne.

 

Ko ko gidan talakawa ne.

 

Shige ki wa mata kitso.

 

Don kuma maigida yak kire ki.

 

Kuma mata sun kire ki.

 

Babu halin shari’a.

A cikin wannan waƙa, makitsiya tana kurara ƙarfin ikonta a fannin kitso. Tana nuna cewa, ita ke da ikon yin yadda ta so da kan wadda take yi wa kitso, ko da kuwa mai mulki ce ko tana da ƙarfin faɗa a ji a cikin al’umma. Wato dai waƙar na nuna hoton yadda mai kitso ke jujjuya kan wadda take yi wa kitso. Wadda ake mata kitson kuwa dole ta bi umarnin mai kitson domin burinta kawai a kammala cikin nasara kuma ya yi kyau.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments