Ticker

6/recent/ticker-posts

3.2.3 Lumu Shege! - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 102)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.2.3 Lumu Shege! 

Wannan waƙa ta karkata ne kan maza masu halin banza ga mata. Kasancewar an yi amfani da sunan Lumu, za ta iya yiwuwa a tarihi wani mai wannan suna ya taɓa yin gagarumin abu makamancin wannan. Ga dai yadda waƙar take kamar haka:

Ina Lumu shege,

Mai malmala ga munta.

 

Kare baƙin bahwade,

Ya hana mu walwala.

 

Mata ku yo aniya,

Bana Lumu ƙwace yakai.

 

Ta masussuki yab biya,

Yat ta da gindi tsaye.

 

Wanga ɗan baƙin mugu,

Ya hana mu walwala.

 

Kare baƙin bahwade,

Mai malmala ga munta,

Ba za ya gwaa hwashe ba.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments