Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
3.1.1 Waƙar Daka Mai Suna Bandaro
‘Yar Aljanna, (2017) ta bayyana wa wannan littafi wani labarin abin kunya da ya faru da mata suka daɗe suna amfani da shi cikin lugude. Ta bayyana cewa, an taɓa yin wata amarya mai rowa. Wata rana sai mijinta ya sayo mata agwagwa domin ta dafa. Gidan kuwa ana zama ne irin na gandu. A maimakon ta dafa a murhun da aka saba dafa abinci, sai ta shiga ɗaki ta kafa murhu a kusurwa guda.
Kafin nama ya gama dahuwa sai kuma wani uzuri ya same ta da ta fita na tsawon lokaci. Abin ka da tsautsayi kawai sai itace ya ci har ya fito daga murhu ya kama ledar tsakar ɗaki. Kan ka ce kwabo ɗaki ya kama da wuta. Nan aka yi kwalala aka zo aka kashe wutar bayan ta yi ɓarna cikin ɗakin.
Bayan faruwar wannan al’amari, sai mata suka juya shi zuwa waƙa, kuma suke amfani da shi yayin lugude. Ga yadda abin yake:
Agwagwa ta ɓararraka ta yi kauyi,
Ba ki san bandoro ya shafe ki ba?
Iya kin yi salla kuwa?
Ta yaya zan yi salla?
Ba ku san bandaro ya shafe mu ba?
Ledar tsakar ɗaki tai shiru,
Ga bandaro ya shafe ta.
Da samira za tai magana,
Sai dish ya hana ta,
Ya ce,
Ba ki san bandaro ya shafe mu ba?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.