Ticker

6/recent/ticker-posts

3.2.2 Bawan Allah - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 101)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.2.2 Bawan Allah 

Wannan ma waƙa ce ta ɗaɓe. Tana ɗauke ne da kalaman tausaya wa talaka, inda ake nuna ba shi da ƙarfin faɗa a ji ko kare kansa daga cutarwar azzalumai. Ga yadda waƙar take:

Bawan Allah,

Talakka bawan Allah.

 

Ba shi da baki,

Balle shi furta kalami.

 

Ba shi ƙafafu,

Balle shi tashi shi tsere.

 

Bawan Allah,

Talakka bawan Allah.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments