Ticker

6/recent/ticker-posts

3.1.4 Ta Gidan Malam Audu - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 99)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.1.4 Ta Gidan Malam Audu

Wannan waƙa ana yin ta ne a cikin lugude. Ta kasance tamkar gaisuwa ce tsakanin masu daka, inda idan ɗaya ta yi gaisuwa sai guda kuma ta amsa mata. Ga yadda abin yake kasancewa:

Ke ta gidan, ke ta gidan,

Ke ta gidan Mallam Audu.

 

Uwar gidan Malam Audu,

Sha lelen Mallam Audu.

 

Ina yininki?

Binta ina yininki?

 

Gaisuwa da aminci,

Yarda ta fi aminci.

 

Hausa tana gaishe ki,

Kin kwana lafiya?

Kin tashi lafiya.

 

Wadda ake lugude da ita za ta ba da amsa kamar haka:

Ke ma kin tashi lafiya?

Ke ma ina gaishe ki,

Kin yini lafiya?

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments