Ticker

6/recent/ticker-posts

3.1.4 Masu Lalura


Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.1.4 Masu Lalura

Masu lalura a nan na nufin wasu mutane da a dare ɗaya suka tsinci kansu cikin wata matsala wadda ta tilasta su neman taimakon jama’a wani lokaci har abin ya kai su ga yin bara domin samun ficewa daga matsalar da suke ciki. Irin waɗannan matsalolin da kan tilasta wasu shiga bara sun haɗa da yankewar guzuri ko sata ko gobara ko ambaliya ko harin ta’addanci ko wata rashin lafiyar da babu abin zuwa asibiti ko faɗuwar gini da sauransu. Da yawa irin waɗannan mabarata da zarar sun sami abin biyan buƙatarsu sukan daina baran, domin da ma kafin wannan mutane ne su masu harakar yi, baran ya riske su ba shiri.

Sai dai a kula da cewa, cikin irin waɗannan mabarata ana samun bar-gurbi waɗanda abin da suke faɗa suna bara da shi duk ƙarya ne[1]. To su irin waɗannan ba su daina bara domin da ma ba abin da suke faɗa ne ya sa su bara ba.



[1]  Akwai wani irin wannan da aka kama yana bara ya liƙa hanjin akuya a cikinsa, ko kuma masu ƙaryar su matafiya ne guzuri ya yanked a sauransu.  

Post a Comment

0 Comments