Ticker

6/recent/ticker-posts

3.1.2 Ana Lugude Ana Mama - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 98)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.1.2 Ana Lugude Ana Mama

Wannan na ɗaya daga cikin waƙoƙin daka da mata kan rera. An fi yin wannan waƙa a gidajen bukin suna (bukin haihuwa). Wannan ne ma ya sa waƙar ke ɗauke da habaici ga kishiya, cewa ana ta raɗe-raɗin mai jegon ba za ta haihu ba, sai kuma ga shi ta ba maraɗa kunya ta hanyar haihuwar santalelen jariri. Ga yadda waƙar ke kasancewa:

Ana lugude ana mama,

Cikin shigifa cikin soro.

 

Mama ba habaici ce ba,

Salon daka a hakan nan.

 

Ga maccen da ba a so ta haihu,

Ta haifi ƙwandamin ɗa namiji.

 

Shugaban daka shi ka daka,

‘Yan tanyo kissa sukai,

Sukus-sukus sai su aje.

 

Gidan Marafa kaji ka daka,

Tarmani na izo wuta.

 

Tarmani na izo wuta,

Angulu ka kirɓa dawo.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments