Ticker

6/recent/ticker-posts

3.1 Masu Bara A Ƙasar Hausa

 

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.1 Masu Bara A Ƙasar Hausa

Mutane ba su taru suka zama ɗaya ba, duk da waɗannan hanyoyi mayalwata[1] na aiki domin samun abinci da arziki da ke birjik[2] a yankin na ƙasar Hausa bai hana a sami wasu waɗanda suka ɗauki bara ya zame masu sana’a ba, wasu ta wani ɗan lokaci kamar almajirai da da gardawa da waɗanda suka faɗa cikin wata lalura ta ɗan lokaci, wasu kuma ta dindindin kamar wasu naƙasassu da masu matattar zuciya. Hanyoyin tattalin arziki ingantattu kamar yadda aka bayyana baya, ya ƙara jawo mabarata zuwa yankin ko bayan ‘yan gida masu baran. Akwai nau’in mabarata dabam-daban a cikin yankin ƙasar Hausa, kamar Almajirai da Gardawa da naƙasassu da masu lalura da masu matattar zuciya. Bayani a kan su zai biyo daki-daki.



[1]  Masu yawa.

[2]  A ko’ina cikin sauƙi.


Post a Comment

0 Comments