𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, malam barka da
warhaka, malam tambayata ita ce, mun karanta hadisai da suke nuna mana cewar
Allah da Manzonsa sun tsine wa namiji mai kamanceceniya da mata, haka ma ita ma
macen, to malam tambayata a nan ita ce shin malam har da macen da ta sanya
kayan mijinta don raha da wasa a tsakaninta da mijinta wanda kuma ba fita za ta
yi da su ba? shin malam ina hukuncin yin hakan? ALLAH ya ƙara wa malam lafiya.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, Matuƙar
Shari'a zta haramta abu da nassi ingantacce kuma bayyananne, to ba ya halasta
mutum ya ce zai kwatanta yin wannan abun don ya daɗaɗa ma wani, saboda haka ba
ya halasta mace ta sa tufafin mijinta don wasa tsakaninta da shi, Ibn Abbas ya
ce: Manzon Allah ﷺ ya la'anci masu kamanceceniya da mata daga cikin mazaje, da
masu kamanceceniya da maza daga cikin mataye" Bukhariy 5885.
A wani hadisin kuma da yake
magana a kan sanya kayan ma ƙuru-ƙuru, wanda Abuhuraira ya ruwaito yana cewa:
"Manzon Allah ﷺ ya tsine wa namiji mai sa kayan mata, da mace mai sa kayan
maza" Abu Dáwud 4098.
Saboda waɗannan dalilai, ba ya
halasta namiji ya sa kayan mata ko na wace ce, haka nan ba ya halasta ita ma
mace ta sa kayan maza ko na wane ne a zance mafi zama dai-dai.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Tambaya Da Amsa Abisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Rubuta tsokaci.