Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Cikin Idda, Sai Wani ya yi Zina Dani, Yaya Zanyi ?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam mijina ya sake ni, bayan na yi tsarki ɗaya, sai rikici ya kaure tsakanin arna da musulmai a garinmu, sai wani arne (Christian) ya dauke ni ya yi zina da ni, yanzu malam yaya zan yi game da idda ta ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To 'yar'uwa ina rokon Allah ya kawowa musulmi ɗauki a Nigeria, wannan mas'alar ta ki malamai sun yi saɓani a kanta, akwai malaman da suka tafi akan dole sai kin yi istibra'i bayan kin gama idda, saidai maganar da tafi zama daidai ita ce : kawai za ki karasa iddarki ne, ba sai kin yi istibra'i ba bayan kin kammala, saboda babbar manufar istibra'i ita ce kubutar mahaifa, hakan kuma zai tabbata idan kika karasa jinane biyun da suka rage miki na iddarki.

Yana daga cikin saukin addinin musulunci kasancewar duk ibadojin da za su iya shiga cikin juna kuma manufarsu ɗaya ce, jinsinsu guda ne, to ɗaya za ta shiga cikin ɗaya, kamar wacce ta yi jima'i sai kuma haila ta zo mata, wanka guda ɗaya ya ishe ta a karshen hailarta.

Duba : Majmu'ul fawa'id na Sa'ady shafi na : 141.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments