Tubalin Ginin Yabo a Waƙoƙin Fada: Tsokaci a Waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo

    Cite this article as: Tijjani, A. & Bello, B.M. (2023). Tubalin Ginin Yabo a Waƙoƙin Fada: Tsokaci a Waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)1, 154-161. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i01.019.

    Daga 

    Amina Tijjani
    Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Zariya.
    07038089907
    aminatijjani(36)@gmail.com

    Da

    Binta Mohammed Bello
    Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Zariya.
    08182651745
    bamallibinta@gmail.com

    Tsakure

    Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo fitaccen makaɗin fada ne da ya shahara a ƙasar Hausa wajen shiryawa da rera waƙoƙin fada da suka ƙunshi yabon sarakuna. Makaɗan fada kan yi amfani da Yabo ne, domin fito da martaba da muhibba tare da kuma kwarjinin sarakuna a bainar jama’a cikin zaɓaɓɓun kalmomi ƙunshe da azanci da ƙawatarwa a waƙa. Manufar wannan muƙala ita ce fito da nau’o’in yabo da Sani Aliyu Ɗandawo ya fi sarrafawa a waƙoƙinsa na sarakuna, musamman waɗanda suke fito da nasaba da jarunta da martabar sarakuna, da kuma iya gudanar da mulki da sauran kyawawan halaye. Muƙalar ta zaɓo waƙoƙi takwas daga cikin ɗimbin waƙoƙin da Sani Aliyu Ɗandawo ya rera a rayuwarsa, a fagen wannan nazari an yi amfani da hanyar da Tsoho (2001) da Ayuba (2012) suka bi wajen ƙwanƙwance yabo a waƙoƙin fada. Muƙalar ta gano cewa makaɗin ya yi amfani da kwalliya da alamci wajen fito da jarunta da buwaya da muhibba ta ubangidansa, sannan ya sarrafa Yabo sifantau da aikatau domin nuna ɗabi’a da halayya saraki. Bugu da ƙari muƙalar ta gano Sani Aliyu Ɗandawo ya sarrafa Yabo dangantau a waƙoƙinsa, domin fayyace nasaba da alaƙa tsakanin sarki da ‘yan majalisansa da fadawansa, da kuma abokan arziƙinsa.

    Fitilun Kalmomi: Yabo, Waƙoƙin Faɗa, Sani Aliyu Ɗandawo

     

    1.1 Gabatarwa

    Yabo babban tubali ne na ginin turke a waƙoƙin fada, makaɗan fada kan yi amfani da Yabo ne, domin fito da kyau ɗabi’a ko halayya ko kuma sifa da kuma nasabar ubangida. Ta wannan hanya ce makaɗan fada sukan yi amfani da Yabo, domin yi wa ubangida hannunka mai sanda game da wasu al’amura da suka shafi gudanar da mulki a masarauta, musamman abubuwan da iyaye da kakanninsu suka yi a lokacin rayuwarsu, wato ta hanyar yabon na lahira don na duniya ya ji haushi. Saboda haka a iya cewa Yabo turke ne babba da makaɗan fada suke isar da wasu muhimman saƙwannin da suka shafi mulki, domin haka waƙoƙin fada ba su cika in babu Yabo a ciki. Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo shahararren makaɗin fada ne da ya ƙware wajen iya sarrafa kalmomi ko gina jimlolin Yabo a waƙoƙinsa.

    Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da nau’o’in Yabo da dama cikin waƙoƙinsa, domin yaba kyawawan ɗabi’u ko halayyar ubangida, ta fuskar jarunta da buwaya da kuma iya gudanar da mulki don daɗaɗawa gwarzo, a ɗaya ɓangaren kuma Yabo kan fusatar da abokan adawa da sa masu tsoro a cikin zuciya. Sani Aliyu Ɗandawo ya sarrafa nau’o’in Yabo da dama cikin waƙoƙinsa, amma wannan muƙala ta nazarci Yabo na kwalliya, da na alamci, da Yabo sifantau da aikatau, da kuma Yabo dangantau da ya ƙunshi dangantaka da iyaye da kakanni, ‘yan majalisa, abokan arziƙi, fadawa.

    2.1 Taƙaitaccen Tarirhin Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo

    Sani ɗa ne shahararren makaɗin fadan nan a ƙasar Hausa makaɗa Aliyu Ɗandawo, an haifi makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo ne a garin Argungu ta jihar Kebbi ta yau a Augusta ga shekarar 1949. Tun yana yaro, ya sami kyakkyawar tarbiyya da girmama na gaba a rayuwarsa. Sani Aliyu Ɗandawo ya yi karatun Muhammadiyya, har ya sauke Al-ƙur’ani mai tsarki, ya ci gaba da karatun littafai daidai gwargwado. Ya fara karatun Boko, amma bai yi nisa ba, sai sana’arsa ta kiɗa ta ɗauke masa hankali ya bari (Gusau,1996 p. 163).

    Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo ya fara koyon kiɗa da waƙa ne a wurin mahaifinsa tun yana ƙasa da shekara goma da haihuwa, kodayake bai fara waƙa ta ƙashin kansa ba, sai bayan mutuwan mahaifinsa Aliyu Ɗandawo, duk da cewa tun yana raye ya haddace wasu waƙoƙi da dama na mahaifinsa. Waƙar da Sani Aliyu Ɗandawo ya fara ta ƙashin kansa ita ce waƙar Sarkin Gabas Attahiru na birnin Yawuri. Ma fi yawan waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo sun fi karkata ga waƙoƙin fada tamkar mahaifinsa Aliyu Ɗandawo, saboda haka tun asali waƙoƙinsa sun fi taɓo al’amuran sarauta. Yakan shirya waƙoƙi ne domin yabon sarki da sauran jinin sarauta, da kuma yin zambo ga abokan hamayya, kodayake daga baya abin ya faɗaɗa, domin ya riƙa sirkawa da wasu waƙoƙi na attajirai, amma duk da haka bai zarce zuwa waƙoƙin noma ko fawa ko wata sana’a ba (Bala, 1982 p. 46) da (Gusau, 1996 p. 167).

    Gusau (1996 p. 165) ya kasa waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo gida biyar kamar haka:

    a.      Waƙoƙin Sarauta waɗanda su ne tushe da asalinsa.

    b.      Waƙoƙin Jama’a waɗanda suka biyo daga baya.

    c.       Waƙoƙin Siyasa

    d.     Waƙoƙin Ta’aziyya

    e.      Waƙoƙin Faɗakarwa

    f.        Waƙoƙin Faɗakarwa.

    Duk da waɗannan nau’o’in waƙoƙin da Sani Aliyu Ɗandawo ya rera bai sanya ya fita daga cikin sunayen manyan makaɗan fada na ƙasar Hausa ba. Gusau ya kawo Sani Aliyu Ɗandawo a cikin makaɗan sarakuna rukuni na biyu, Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo ba ya yin waƙa kai tsaye, sai ya zauna ya shirya ta, tare da taimakon mataimakansa, domin ta dace da wanda yake wa waƙa, sanin abubuwan da suke faruwa a fada da ƙasa baki ɗaya yana taimaka masa wajen ƙulla ɗiyan waƙa ta yi tsawo. Sani Aliyu Ɗandawo ya fi yin waƙoƙinsa a yammacin juma’a wato Alhamis da daddare, sai kuma lokacin bukukuwan sallah babba da kuma ƙarama (Gusau, 1996 p. 165-168). Allah ya yi wa Sani Aliyu Ɗandawo rasuwa ne a yammacin ranar Lahadi 4 ga watan Afrilu, 2016 (Salihu, 2016) a cikin (Lawal, 2016 p. 265).

    3.1 Yabo a Waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo

    Yabo a Hausa ya ƙunshi kalma ko yankin Magana ko jimlar da aka yi amfani da ita wajen yaba wa gwarzo cikin kwalliya ko kuma alamci, ta hanyar sifanta su da wasu ƙarfafan dabbobi ko wasu abubuwa ko kuma yanayi da yake alamta tsoro ko firgici. A wannan Yabo ne makaɗan kan sifanta jarumi, da cicciɓa shi tare da fito da ƙimarsa a idon alummarsa. Har wa yau Yabo kan ba makaɗan damar bayyana kyawawan ɗabi’u ko halayen sarki, domin ƙarfafa masa gwiwa ya ci gaba da kyautata rayuwar talakawansa (Tsoho, 2001 p. 145-6) da (Ayuba, 2012 p. 259). Yabo yana da matuƙar tasiri a waƙoƙin fada, domin ta wannan hanya ce makaɗi yake yabon ubangidansa ya tsima shi ya yi kyautar isa, wani lokaci irin wannan kyauta kan zarce, sarki ya yi da kansa shi kaɗai, ‘yan’uwansa da abokan arziƙi da sauran masoya ma kan yi a madadinsa (Ayuba, 2012 p. 260).

    Umar (1985 p. 48) a cikin Tsoho (2001) ya ruwaito cewa wasu fitattun abubuwa da mawaƙa suka fi amfani da su wajen yabon iyayen gidansu, sun haɗa da: Giwa wadda take nuna ƙarfi da kammalallen iko, zaki da yake nuna ƙarfi da jarunta da kuma dattijantaka, sai kuma doki da ke nufin tasiri da arziƙi, kura kuwa tana nuna haɗama ce da zalunci da kuma barazana, jaki ya nuna wawanci, raƙumi kuwa juriya yake nufi, dila kuwa ya nuna wayau ne, biri kuwa ɓarna, mujiya baƙin jini, ja ke nuna matsala ko jaruntaka, ko tsanani baƙi, ko kuwa rashin sa’a, kore alama ce da take nuna ƙaruwa, ruwa kuwa tsafta da tsarki da ƙarfi da ci gaba.

    Ke nan yabo hanya ce da makaɗi yake kambama ko wasa ubangidansa da wata kyakkyawar sifa ko ɗabi’a ko kuma halayya, domin ya daɗaɗa masa rai da makusantansa ko masoyansa ya yi kyautar isa ko kuma a yi kyautar isa dominsa. Makaɗan fada su suka fi amfani da Yabo a waƙoƙinsu, domin su fito da ƙimar ubangidansa ga talakawansa da ma sauran sarakuna. Tsoho (2002) ya nuna cewa makaɗa fada kan yi amfani da Yabo ne ta fuskar nuna jarunta ko ƙarfin ikon sarki da girmamawa da haƙuri da siga da ɗabi’a da dangantaka da sheɗanci da tsoratarwa da ɗaukaka da tsaro da ɓarna da horo da jin daɗi da kuma hikima.

    Ke nan a iya cewa a Yabo ne makaɗi kan yi amfani da kwalliya ko alamci da nufin samun zarafin ɗaukaka gwarzo zuwa ƙololuwar daraja da ƙimar da ba kowa ne zai iya samunta ba, misali inda suke kwatanta ubangida da giwa domin su gwada cewa shi ne sarki mai cikakken iko da babu wanda zai iya ja da shi a faɗin ƙasarsa. In kuma jarunta ce ko ƙarfi sukan kwatanta shi ne da zaki. Wato duk ɗabi’a ko sifa ko kuma halayyar da suke so su kambama wa gwaninsu, sai su ɗauki wata fitacciyar dabba ko wani abu da Hausawa suka sakar masa wannan abu, domin kai ubangidansu ƙololuwar daraja. Da wannan ne muƙalar ke jaddada cewa akwai alaƙa tsakanin Yabo da kirari da kuma kambamar zulaƙi, domin dukkansu sun haɗu a manufa guda, manufar kuwa ita ce koɗa mutum da kai shi ƙololuwar daraja, domin karfafa shi ya yi abin da buƙata, ko da ba shi da niyyar aikata haka.

    3.1.1 Yabo na Kwalliya

    Dama babban manufar Yabo ita ce daɗaɗawa ubangida da iyalansa da abokan arziƙin da ma masoyansa, in da hali a ƙasƙantar ko muzanta abokan hamayyarsa. Saboda haka idan makaɗi ya zo sarrafa wannan salo yakan yi amfani da wasu dabbobi ne ƙarfafa, ko abubuwa masu ƙarfin gaske da wasu iskoki don nuna iko da ɗaukakar ubangida. Wasu daga cikin dabbobi da abubuwan da makaɗan kan yi amfani da su sun haɗa da: giwa da zaki ɓauna da amale da bajimi da damisa da ruwa da aradu da aljanna da dodo da maye da bangon-tama da gamji da sauransu. Yawanci sukan yi amfani da sunayen waɗannan dabbobi ko abubuwa, domin sifanta da sarki kai tsaye (Tsoho, 2001 p. 4-5) da (Ayuba, 2012 p. 260). Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da Yabo na kwalliya domin ya nuna fifikon ƙarfi tsakanin ubangidansa Madawaki da magabtansa, inda yake cewa:

    Jagora: kare bai ja da kura.

    Karɓi: Don ba ƙarfinsu ɗai ba.2

    Jagora: Wani ya kama hargini ya ɗaukai da banza,

     Wani ya kama damisa dut ta yamutce shi.2

    ‘Y/Amshi: Bai kai wargi ba Audu,

     Mu zo mu ga Madawaki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Madawaki Audu)

     

    Idan aka lura da wannan ɗiya Sani Aliyu Ɗandawo ya kwatanta gwaninsa Madawaki Audu da kura, yayin da ya kwatanta abokin hamayyarsa da kare. Makaɗin ya yi haka ne domin ya nuna cewa fifikon da ke tsakanin kare da kura, shi ne tazarar da ke tsakanin ubangidansa da ‘yan adawa. Sanannen abu ne cewa kura ta ɗara kare ƙarfi nesa, domin haka Madawaki ya fi ƙarfin abokan adawansa nesa. In har suka kuskura suka gwabza da shi, zai nuna masu shi jarumi ne, zai gama da su, domin ƙarfinsa da buwayarsa sun ɗara na su. Irin wannan kwatancen ne ya fito ɗiya ta gaba tsakanin damisa (Madawaki Auda) da hargini (abokan hamayyarsa). Wannan Yabo na kwalliya ya fito da jarunta da ƙarfin iko Madawaki Audu a kan abokan adawa, ta hanyar nuna tazarar ƙarfi da fifikon daraja a tsakaninsa da magabta. Irin nau’in wannan yabo ya fito a ɗiyar waƙar sarkin Maska inda yake cewa:

    Jagora: Ina Giwa mai karya itace, Sarkin sarakuna na Maska.

    Karɓi: Gwanki sha bara uban Tukura Garba, ko sun yi harbe-harbe banza,

     Yau Rabbana yana ciki nai.

    ‘Y/Amshi: Giwa buwayi masu ja ma,

     Sarkin sarakuna na Maska,

     Mai martaba na madawaki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Sudan na Kwatangora)

    A nan Sani Aliyu Ɗandawo ya yabi sarki ne ta hanyar kwatanta shi da giwa da gwanki domin ya nuna ƙarfi da gagara ta sarkin sarkin Sudan na Kwantagora a cikin ‘yan’uwansa sarakuna da talakawansa ko al’umma baki ɗaya. giwa a matakin farko ta fito da ƙarfinsa, a mataki na biyu kuma ta fito da buwayarsa a cikin sarakuna, wato ya duk wanda ya kara da shi zai koka. A ɗaya ɓangaren kuma an kwatanta shi da gwanki domin a fito da gagararsa a tsakanin ‘ya’yan sarki, wato duk adawarsu gare shi, ba ya hana ci gaba da mulki da kasancewa sarki, duk ƙiyayyarsu ba ya hana shi komai, sai ci gaba.

    3.1.2 Yabo na Alamci

    Kamar Yabo na kwalliya shi ma yana fito da matsayi ko bajintar ubangida ne ta hanyar misalta shi da wani abu ko wata alama da za ta iya wakiltar yanayi ko matsayin gwanin da makaɗi yake yabo. A nan makaɗi kan alamta ubangidansa ne da wata alama ko wani abu fitacce mai muhimmanci gaske mai nuna ƙarfi, wanda zai fito da zatin ubangida ko kambama shi ta fuskar jarunta ko iya mulkin jama’a ko kuma kwarjini a idon al’umma. Za a ga misalign wannan Yabo na alamci a ɗiyar waƙarsa da ke cewa:

    Jagora: Gwanki sha bara na Cancangi,

     Namijin tsaye bai taɓa shakka ba.

    Karɓi: Ya bindiga mai ta’adin ƙarhi,

     Harsashi dole a kauce ma.

    ‘Y/Amshi: Na Amadu mai kwana kyauta,

     Nadabo ƙanin Haji Cancangi.

    (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Nadabo ƙanin Cancangi)

    A wannan ɗiya Sani Aliyu Ɗandawo ya alamta gwarzonsa ne da wasu muhimman abubuwa da suke nuna ƙarfi kamar bindiga da harsashi, sannan ya alamta shi da namijin tsaye da ke nufin tsayayye ko kuma jajurtaccen mutum, mai ƙarfi da kammalallen iko a cikin jama’a. Bindiga da harsashi a nan suna alamta ƙarfi da jarunta ta gwarzon da ake yi wa yabo, sannan harsashi yake fito da matsayinsa ga abokan adawansa, wato ya gagare su duk wanda ya ja da shi, shi ne yake ƙasa, domin buwayarsa a idon jama’a. Irin wannan Yabo ya fito a waƙar Sarkin Minna, Sani Aliyu Ɗandawo cewa ya yi:

    Jagora: Farin wata sha kallo, Ummaru jikan Ummar.

    Karɓi: Kai kowa yake murna,

     Ya ishe ma ya yi kallo.

    ‘Y/Amshi: Ummaru ja a sakar ma,

     Minna zan sheƙe aya ta,

     In ga Faruƙu sadauki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Minna Ummar Faruƙ)

    A nan Sani Aliyu Ɗandawo ya alamta sarkin Minna ne da farin wata, domin ya nuna farin jininsa ga al’ummarsa. Wannan kalmar Yabo ta farin wata fitacciya a tsakanin makaɗan fada, wanda suke amfani da ita domin su nuna kwarjini da karɓuwa da kuma farin jinni gwanayensu a cikin waƙa. Saboda haka a iya cewa Sani Aliyu Ɗandawo ya yi haka ne ya yabi farin jinni da karɓuwa da sarkin Minna yake samu a jama’arsa. Kuma wannan ya fito da kwarjininsa a cikin sarakuna.

    3.1.3 Yabo Sifantau

    Wannan nau’in Yabo ne da musamman makaɗan fada suke amfani da shi, domin su bayyana kyawawan sifa da halaye da ɗabi’un gwanayensu, wato waɗanda suke wasawa a waƙa. Yayin wannan Yabo makaɗan kan yi amfani da wasu fitattun kalmomin Yabo da suke bayyana waɗannan sifofi ko halaye ga waɗanda suke wa waƙa. Sukan kira ubangida da: Sadauki da ke nuna shi jarumi ne, ko kuma Mashasha domin nuna tsananin kyauta, da kuma Katakore ke nuna ƙato da sauran makamantansu (Tsoho, 2001:6) da (Ayuba, 2012:261). Wannan nau’in Yabo ya fito a ɗiyar waƙar Sarkin Sudan na Kwantagora, inda Sani Aliyu Ɗandawo yake cewa:

    Jagora: Sa’idu Sadauki ɗan Sadauki,

    Karɓi: Ka zama gargaƙi wandon ƙarhe,

     Kwas saka bai shirin zama.

    ‘Y/Amshi: Giwa buwayi masu ja ma,

     Sarkin sarakuna na Maska,

     Mai martaba na madawaki.

    (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Sudan na Kwantagora)

    Alhaji Sani Aliyu ya yi amfani da Kalmar Yabo ta sadauki ne a nan, domin ya nuna jaruntar gwaninsa, kuma ya ƙara da cewa sadaukantakar tasa ‘yar asali ne, gada ya yi wajen iyayensa, wato shi sadauki ne, kuma ɗan sadauki. saboda haka ya ci gaba da koɗa shi da kuma tsoratar da magabtansa. Ya kira shi da gargaƙi wandon ƙarfe, domin haka duk wanda ya kuskura ya ja da sarki, babu shakka zai gane, ya kara da jarumi, sarki zai ga bayansa, domin sarki jaruntarsa, dama ya gaji jarunta tun daga iyaye. Haƙiƙa waɗannan kalmomin Yabo sun sifanta sarkin Maska Sa’idu da jarunta, domin fito da ƙimarsa a idon ‘yan’uwansa sarakuna da talakawansa. Yabo sifantau ya bayyana a wannan ɗiya da ke tafe.

     Jagora: Ashe Giwa in taɗ ɗau kaya, in ta aje su ba mai ɗauka,

     Tun ran da Hashimu yat tashi Yalwa da ‘yan kasuwa da ‘ya’yan sarki,

     Ban sami wanda yaɗ ɗaukan ba,

     Bana ga ƙanin Bala na samu,

     Ku riƙe ni gaskiya ni Alhaji,

     Amma saboda girman Allah.

     Karɓi: Amadu ƙanin Bala ya ɗauka.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Amadu ƙanin Bala)

    Idan aka lura da wannan ɗiya za a gane cewa tun farkonta Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo ya riƙa wasa gwaninsa giwa, domin kasancewarta dabba da ta shahara wajen ƙarfi. Sai dai a nan Sani Aliyu Ɗandawo ya kwatanta gwanin ne, da ƙarfi amma na tattalin arziƙi, wato ya nuna gwaninsa a garin Yalwa shi ya fi kowa ƙarfin tattalin arziƙi da zai ɗauki ɗawainiyarsu. Kamar yadda giwa fi sauran dabbobin dawa ƙarfi.

    Jagora: Saboda Gogarma mai toya matsafar arna,

    Karɓi: Ɗan iyan Zazzau ya ba ni dubun nairori.

    ‘Y/Amshi: Ture-haushi sadauki Alhaji sarkin Zazzau,

     Bi-da-arna jikan Sambo sadaukin sarki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Zazzau Shehu Idris)

    Kamar a misalai na baya, Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da Kalmar Yabo ce ta gogarma, domin ya sifanta jarunta ta mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da buwayarsa a cikin sarakuna. Amfani da wannan kalma ya nuna yadda sarki ya buwaya a duk faɗin ƙasarsa.

    3.1.4 Yabo Aikatau

    Wannan nau’in Yabo shi ya fi yawa a cikin tarin Yabo da ake da su a Hausa. Yawanci irin waɗannan kalmomin Yabo harɗaɗɗun sunaye ne, waɗanda ake haɗa aikatau da suna, ko ‘yan asalin aikatau, kalmomin suna nuna ayyukan da ubangidansu ya yi ne, ko kuma ake fatar ya yi a gaba. An riƙa amfani da waɗannan kalmomi ne lokacin da ƙasar Hausa ta kasance cikin yaƙe-yaƙe na cikin gida, kodayake an ci gaba da amfani da waɗannan sunaye domin yabon sarakuna, musamman idan makaɗan na buƙatar nuna jaruntar ubangidansu a cikin waƙa (Tsoho, 2001:8-9) da (Ayuba, 2012:261-262). Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da Yabo aikatau a ɗiyar waƙar Sarkin Zazzau Shehu Idris, inda yake cewa:

    Jagora: Saboda Gogarma mai toya-matsafan arna,

    Karɓi: Ɗan iyan Zazzau ya ba ni dubun nairori.

    ‘Y/Amshi: Ture-haushi sadauki Alhaji sarkin Zazzau,

     Bi-da-arna jikan Sambo sadaukin sarki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Zazzau Shehu Idris)

    Waɗannan kalmomin Yabo da Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da su a wannan ɗiya wato toya-matsafa da take nuna jarunta da buwaya, ture-haushi da take bayyana kirki da karimci da kyautatawar gwaninsa, sai kuma Kalmar bi-da-arna da take ƙara fito da buwayarsa da ƙarfin iko a ƙasarsa. Haƙiƙa waɗannan kalmomi da aka yi Yabo da sun fito da zatin sarki da ƙimarsa ga al’ummarsa da yake wa jagoranci. Domin za a iya fahimtar cewa sarkin ya ƙasaita, yana iya zartar da ikonsa ga kowa a cikin jama’arsa ba tare da shayi, saboda shi jarumi ne, kuma karimi ne, wajen kyautatawa. Har ila yau, za a ƙara ganin irin waɗannan kalmomin Yabo na aikatau a cikin wannan ɗiya da ke cewa.

    Jagora: Zaki kake ci-da-ƙarfi mai karya mutum da ƙarfi.

    Karɓi: Shi ke zabga ƙarhi, mutum bai kai garai ba.

    ‘Y/Amshi: Bai kai wargi ba Audu,

     Mu zo mu ga Madawaki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Madawaki Audu)

    Kamar ɗiyar da ta gabata, Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da Kalmar Yabo ta aikatau ce ta ci-da-ƙarfi a nan, domin ya gwada buwayar gwaninsa ta hanyar fifita a kan kowa, wato gwaninsa yana da ƙarfin da babu wanda zai iya karawa da, domin jarumi ne. Makaɗan fada sau da yawa sukan yi irin wannan yabo ne, domin daɗaɗa wa ubangidansu, da kuma tsoratar da magabtansa. Sani Aliyu Ɗandawo ya bi sahun sauran makaɗan fada, wato ya yabi gwaninsa, daidai lokacin da yake tsoratar da abokan adawan gwaninsa. Wato irin hikimar da ake cewa ka yabi na lahira, domin na duniya ya ji haushi.

    3.1.5 Yabo Dangantau

    A ƙasar Hausa an ɗauki sarki uba ne ga kowa, saboda haka ake amince masa ya tafiyar da mulkin jama’arsa baki ɗaya (Ayuba, 2012:262). Iyaye da kakanni kuwa suna da matuƙar muhimmanci ga sarki, domin ana ganin albarkacinsu ne ya sami sarauta, kuma yake kasancewa sarki, musamman ma in ya kasance sun shahara sosai, ta fuskar mulki ko malanta ko kuma jarunta, daga na sai ‘yan majalisar sarki da danginsa da gidajen sarautu wani lokaci har ma da talakawansa, sai kuma aminan sarki da abokan arziƙinsa. Waɗannan rukunin mutane ne makaɗan suka fi ƙarfafawa wajen yabonsu, domin su nuna alaƙarsu da matsayinsu da kuma soyayyarsu ko kusancinsu ga sarki (Tsoho, 2001:8-9) da (Ayuba, 2012:262). Ayuba (2012) ya kawo nau’in Yabo dangantau huɗu a cikin Bakandamiyar Abubakar Akwara (Bahagon Gulbi) da suka haɗa da: Dangantaka da kakanni da iyaye da dangantaka da ‘yan majalisa da dangantaka da abokai da kuma dangantaka da fadawa. Wannan muƙala za ta yi amfani da tsarin Ayuba (2012), saboda haka za a yi nazarin Yabo dangantau a waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo kamar haka:

    3.1.5.1 Dangantaka da iyaye da kakanni

    A wannan rukuni makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo kan yabi ubangidansa ne ta hanyar danganta shi da wasu gawurtattun sarakuna da suka gabaci gwaninsa, domin ya nuna cewa ubangidansa ɗan asali ne, ba taka-haye ba, domin sarautar ma ko jarunta ko kuma ƙasaitarsa ta gado ce. Dubi yadda Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da dabara a waƙar Sarkin Zazzau Shehu Idris domin ya wasa sarki. Ga ɗiyar waƙar kamar haka:

    Jagora: Jikan Sarki Kwasau,

     Jikan Sarki Sambo,

    Karɓi: Shehu gwarzon Abdullahi sadaukin Sarki.

    ‘Y/Amshi: Ture-haushi sadauki Alhaji sarkin Zazzau,

     Bi-da-arna jikan Sambo sadaukin sarki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Zazzau Shehu Idris)

    A wannan ɗiya Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da wannan dangantaka na domin ya nuna cewa sarkin Zazzau ya gaji sarautar ce da tushe, wato kakanninsa sarki Kwasau da sarki Sambo sun yi sarauta a Zazzau, yau shi ma ya bi sahun, ya zama sarki. Irin wannan Yabo yana ƙara kwanzarta sarki ya ƙara ƙaimi da ƙwarin gwiwa a gudanar da mulki, domin ya ji cewa iyayensa da kakanninsa duk sarakai ne, saboda haka shi ɗan asali ne a sarautar Zazzau, ba taka-haye ba.

    3.1.5.2 Dangantaka da ‘Yan Majalisa

    A ƙasar Hausa ‘yan majalisan sarki suna da matuƙar muhimmanci a gudanar da mulki, domin suna mataimakan sarki a wasu ɓangarori kuma mashawartansa a gudanar da mulki baki ɗaya. Saboda haka wasun sarki bai yi sai da taimakonsu. Makaɗan fada kan riƙa saƙa sunayen waɗannan sarautu ne da nufin nuna kusancinsu da sarki. wannan yana ƙara soyayya a tsakaninsu da kuma ɗaukaka darajarsu a idon hakimai ‘yan’uwansu da ma talakawa baki ɗaya (Tsoho, 2001:11) da (Ayuba, 2012:263). Wannan nau’in Yabo ya yi tasiri a waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo a ɗayar waƙar da ya yi wa Sarkin Sudan na Kwantagora, inda yake cewa:

    Jagora: Uban Sardauna, Uban su Barade,

     Uban Tukura da Magajin Rafi.

    Karɓi: Jigo na Ɗanmadami sarki.

    ‘Y/Amshi: Giwa buwayi masu ja ma, Sarkin sarakuna na Maska,

     Mai martaba na Madawaki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Sudan na Kwantagora)

    Idan aka lura da waɗannan sunayen mutane da Sani Aliyu Ɗandawo ya ambato cikin wannan ɗiya za a fahimci cewa sun danganci manyan ‘yan majalisan sarki ne, domin da jin Sardauna ko Tukura ko Magajin Rafi ko kuma Ɗanmadami duk manyan sarautu ne da suke da muhimmanci a majalisar sarki. Sani Aliyu Ɗandawo ya ambaci sarautunsu ne, domin ya yabi irin kusanci da dangantaka ta ƙad-da-ƙud a tsakaninsu da sarki. Makaɗin ya yi haka ne domin ya ƙara ɗaukaka darajarsu da ƙimarsu ga sarki, sarki ya ci gaba da riƙe su da mutunci, domin shi ne jigon rayuwarsu. Haka kuma wannan ya nuna irin ƙwarewar sarki wajen gudanar da mulki ta hanya ƙulla kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da ‘yan majalisarsa, wato sun ɗauki sarki uba, shi kuma ya ringume su a matsayin ‘ya’yansa.

    3.1.5.3 Dangantaka da Abokan Arziƙi

    Wannan nau’in Yabo ne da makaɗan fada kan riƙa yabawa abokan sarki tun ƙuruciya ko kuma bayan girmansa, wasu ma bayan ya sami sarauta, irin wannan Yabo yana nuna zumunci ne da kuma alaƙa ta ƙud-da-ƙud a tsakaninsu (Ayuba, 2012:263). Har ila yau a irin wannan Yabo makaɗan kan Ambato wasu sarakuna a wasu ƙasashen daban, domin su nuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu da sarki (Tsoho, 2001:11-12).

    Sani Aliyu Ɗandawo ya riƙa amfani da wannan hikima, domin yabon wasu abokan arziƙin sarki da zumunci ko kusanci a tsakaninsu. Ya yabi abokan arziƙin sarkin Sudan na Kwantagora a ɗiyar waƙarsa da ke cewa:

    Jagora: Mai ƙarfi baban su firezdan,

     Jan zaki baban Gadanasko,

     Zaki baban Sani Bello,

     Baban Janar Muhammadu Sarki,

     Yaya yake jikan Atiku,

     Baban su Garba duba Sarki.

    ‘Y/Amshi: Giwa buwayi masu ja ma, Sarkin sarakuna na Maska,

     Mai martaba na Madawaki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Sudan na Kwantagora)

    Wannan ɗiya ta nuna alaƙar da ke tsakanin sarki da wasu muhimman mutane a ƙasarsa, alaƙar kuwa ita ce, shi sarki ne wato uba ne ga kowa komai girman mutum da muƙaminsa a inda ya fito, sarki shi ne ubansa da wannan ne Hausawa kan masa kirari da Sarki uban kowa, sarakuna iyayen ƙasa ne. Sani Aliyu Ɗandawo ya nuna irin alaƙa da ke tsakanin sarki da abokan arziƙinsa, wannan ke gwada irin kyakkyawar mu’amular da take tsakanin sarki da jama’ar ƙasarsa. Ke nan Sani Aliyu Ɗandawo ya yabi sarki ne da iya kyakkyawar mu’amula da abokan arziƙi, domin ya ƙasa danƙon soyayya a tsakaninsu.

    3.1.5.4 Dangantaka da Fadawa

    Fadawa tamkar ‘yan majalisan sarki ne, sai dai su ba su kai ‘yan majalisa ƙarfi wajen zartar da iko ba, domin su aikinsu ya fi ƙarfi wajen yi wa sarki hidimomi da ayyukan da suka shafi fada. Saboda haka fadawa suna da tasiri sosai wajen zartar da adalci ga mai mulki. Ambaton sunayensu a waƙa kan ɗaukaka matsayinsu da ƙarfafa masu gwiwa game da hidimar da suke wa sarki, domin sarkin ba ya yi, sai da su, kamar yadda su ma ba sa yi, sai da shi. Ke nan alaƙar da ke tsakaninsu alaƙa ce makusaci ta ƙud-da-ƙud, ambaton zai ƙara fito da kusancin da ƙara soyayya a tsakaninsu (Tsoho, 2001:12) da (Ayuba, 2012:263). Kasancewar Sani Aliyu Ɗandawo ƙwararren makaɗin fada ya riƙa amfani da wannan Yabo domin ƙarfafa wa Bafade gwiwa da kuma ƙara danƙon soyayya tsakaninsa da sarki. za a ga nau’in wannan Yabo a ɗiyar waƙar:

    Jagora: Uban zagi na mai fada,

    Karɓi: Ginshiƙi na alƙali.

    ‘Yan amshi: Mai tawakkali Musa,

     Bargu zani gun Sarki.

     (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Bargu Musa)

    Zagi da sarkin fada da kuma Alƙali manyan fadawan sarki ne da suke da tasiri wajen tafiyar da harkokin fada, wannan ne yasa Sani Aliyu Ɗandawo ya riƙa yayata soyayyarsu da sarki da kusanci, irin wannan yabo yakan ɗaga darajarsu a idon jama’a da kuma ƙarfafa danƙon soyayya ga sarki.

    4.1 Kammalawa

    Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo ƙwararren makaɗin fada ne, day a ci moriyar sarrafa kalmomin Yabo da sigoginsa ta fuskoki da dama. A ƙarshe muƙalar ta gano wasu batutuwa kamar haka:

    Muƙalar ta gano cewa makaɗin ya yi amfani da Yabo ne, domin yabo ko jinjina ko kuma kwanzarta jarunta da buwaya da kuma ƙasaitar ubangida.

    Haka kuma muƙalar ta gano Yabo a waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo tamkar kirari ne ko kambamar zulaƙe, domin makaɗin kan amfani da shi ne, yayin da ya zo tsima ubangida da koɗa shi da isar baka da kuma razanar da abokan hamayya.

    Har wa yau muƙalar ta gano cewa sanin tarihin saraki da masarauta kan taimaka wajen fito da nasabar saraki da dangantakarsu da wasu mutane a ciki da wajen masarauta.

    Bugu da ƙari muƙalar ta ƙara tabbatar da cewa Sani Aliyu Ɗandawo kamar sauran makaɗan fada yana kwalliya da wasu dabbobin dawa ne a waƙoƙinsa, domin ƙawata waƙarsa da fito da zatin saraki ƙuru-ƙuru a idon jama’a. Misali; Zaki ya nuna ƙarfi, idan kuma aka ce, jan zaki ƙarin daraja ne, kamar giwa da ke nuna ƙarfi na jarunta da kuma tattalin arziƙi da buwaya da kuma cikakken iko, gwanki kuwa kan nuna buwaya da gagara ta fuskar tsaro. sannan makaɗin kan yi da wasu ƙananan dabbobi domin ya fito da fifikon ubangida a kan abokan hamayya. Misali; kare da kura, ko kuma hargini da damisa, wannan na nuna fifiko ne a fili domin mai sauraro ya gane matsayin gwaninsa.

    Daɗin daɗawa Sani Aliyu Ɗandawo ya yi amfani da wasu abubuwa domin fito da ƙarfi na jarunta da iko ko kuma martaba da kwarjini, misali; bindiga da harsashi da goga da gargaƙi da gogarma da kuma namijin tsaye, yayin da ya alamta farin jinin saraki da farin wata.

    Haƙiƙa Yabo ya yi tasiri a waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo, kuma ya taimaka wa waƙoƙinsa wajen ƙawata waƙa da cim ma nasara wajen saƙon da yake ƙoƙarin isar wa ga masu sauraro.

    Manazarta

    1.      Ayuba, A. (2017). Fada a Waƙar Iko: Nazarin Bagire a Tunanin Bahaushe. Muƙalar da aka gabatar a Taron Ƙasa da Ƙasa a kan Hausa a Jiya da Yau da Gobe. Zariya: Sashen Harsuna da Al’adun Afirka. Jami’ar Ahmadu Bello.

    2.      Ayuba, A. (2012). Zuga da Yabo: Matakan Yabo a Bakandamiyar Abubakar Akwara. Champion of Hausa Cikin Hausa. A Festchift Honour of Dalhatu Muhammad. Ed. Amfani at el. Zaria: ABU Press. Pp. 254-264.

    3.      Bala, I. M. (1982). Sani Aliyu Ɗandawo da Waƙoƙinsa. Kudin Digirin Farko, Sashen Harsunan Nijeriya da Afurka. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

    4.      CNHS (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

    5.      Daura, R. J. (2012). Sarautun Ƙasar Daura da Muhimmancinsu ga Hausawa. Champion of Hausa Cikin Hausa. A Festchift Honour Of Dalhatu Muhammad. Ed. Amfani at el. Zaria: ABU Press. Pp. 468-473.

    6.      Gusau, S. M. (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

    7.      Lawal, A. (2016). Kambamen Zulaƙe a Waƙoƙin Makaɗa: Tsokaci a Waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo. Argungu Journal of Language Studies. Sokoto: Hussaini Printers, Ɓol. 2. Pp.265-272.

    8.      Tsoho, M. Y. (2001). Tubalin Ginin Yabo: Tsokaci kan Yabo a Waƙoƙin Iko. Department of Nigerian and African Languages, Zaria: Ahmadu Bello University.

    9.      Tsoho, M. Y. (2002). Eulogues: The Bulding Blocks of Hausa Praise Songs. Unpublished Ph.D Dessertation. Department of Nigerian and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello University.

    10.  Yahaya, I. Y., Sani, M. Z., Gusau, S. M., ‘Yar’aduwa, T. M. (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi Na Uku. Ibadan: University press.

     Get the full PDF here:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.