Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Mutum Na Cikin Matsananciyar Damuwa Mene Ne Ya Kamata Ya Yi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, idan mutumun na cikin matsanantchiyar damouwa mi ya kamata ya yi dan magance ta? Dan Allah kumin kokari na samu amsa da wuri.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, Ibn Mas'ud Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah ya ce: "Wata damuwa ko baƙin ciki ba sa taɓa samun mutumin da ya karanta wannan addu'ar, face Allah ya tafiyar masa da wannan damuwa da baƙin ciki, kuma ya canja masa da kwaranyewar damuwar:

"اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ وَابْنُ عَبْدِكَ وَابْنُ أَمَتِكَ ، نَاصِيَتِي بِيَدِكَ ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ ، أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ ، سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ ، أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ ، أَوْ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ: أَنْ تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي ، وَنُورَ صَدْرِي ، وَجِلَاءَ حُزْنِي ، وَذَهَابَ هَمِّي ؛ إِلَّا أَذْهَبَ اللَّهُ هَمَّهُ وَحُزْنَهُ ، وَأَبْدَلَهُ مَكَانَهُ فَرَجًا".

MA'ANA:

"Ya Allah ni bawanka ne, ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka, makwarkwaɗata (maɗigata) a hannunka take, hukuncinka zartacce ne a kaina, kuma ƙaddararka a gare ni mai adalci ne, ina roƙonka da dukkan sunayenka, wanda ka ambaci kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da shi ga wani daga cikin halittarka, ko ka keɓance kanka da saninsa a cikin ilimin fake (gaibu) da ke wurinka, ka sanya Alƙur'ani ya zama daɗi ga zuciyata, ya zama haske ga ƙirjina, ya zama kwaranyewa ga baƙin cikina, ya zama mai tafiyar da damuwata".

A ƙarshen hadisin an ruwaito cewa Sahabbai sun tambayi Manzon Allah cewa; shin ba ma koyi wannan addu'ar ba? Sai ya ce: "Tabbas, ya kamata wanda ya ji addu'ar nan ya koye ta"".

Musnadu Ahmad (3712), Sahihu Ibn Hibban (972).

Wanda ba zai iya yi da Larabci ba ya yi da Hausa.

FA'IDOJIN WANNAN HADISI:

1. Idan damuwa da baƙin ciki suka dami mutum to ya lizimci wannan addu'ar.

2. Yawan karanta Alƙur'ani yana taimakawa wajen yaye baƙin ciki da damuwa.

3. Allah kaɗai ne yake iya yaye wa mutum baƙin ciki da damuwa ba waninsa ba.

4. Duk idan baƙin ciki da damuwa suka matsa wa mutum ya yi addu'a ne, ba zuwa gidan boka ko ɗan tsubbu ba, musamman ma wannan addu'ar.

5. Idan mutum ya sami labarin wannan addu'ar shi ma ya yi ƙoƙarin sanar da waninsa.

6. Sahabbai suna ba da himma wurin koyon abin da Annabi yake koyar da su, kuma ba sa rowar sanar da al'umma ilimoman da suka koya a wurin Manzon Allah . Da dai sauran fa'idoji da dama.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments