For Referincing: Sani, A-U. (2023). Damar Tuba. Ɗaukar Jinka, p. 133-147. Kangiwa Multimedia and Communications Ltd.
DAMAR TUBA
Na
Abu-Ubaida
Sani
Email: abuubaidasani5@gmail.com
Phone: +2348133529736
La’asar sakaliya ce. Zafin rana ya fara raguwa. Duniya ta
yi wani daɗi musamman da yake na fara fita daga cikin hayaniya. Natsuwa
da kwanciyar hankali suka lulluɓe ni, kamar dai yadda al’amarin yake a duk lokacin da na
kama hanyar fita bayan gari domin shan magungunan da za su rage mini damuwoyin
duniya. A nan babu hargowar mutane. Babu wanda zai faɗa mini
wata maganar da za ta sosa mini rai. Daga ni sai waƙoƙin da
tsuntsaye suke rerawa.
“Allah
sarki, su kam tsuntsaye babu ruwansu da wata matsalar rayuwa. Za su je wurin da
suka ga dama a sararin samaniya, kuma su ci su sha abin da suka ga dama ba tare
da fuskantar wata tsangwama ba. Ni kuwa kullum Abubakar sai ya takura mini cewa
duk abin da nake ɓoye wa mutane, to ba halin ƙwarai ba ne...” Zuciyata
ce ke wannan saƙe-saƙe. To amma ni ai nakan je jeji ne kawai don samun natsuwa
ba don ba na so a ga na sha wani abu ba. Ko da wannan iƙirarin gaskiya ne ko saɓaninta,
da ita nake kau da maganar Abubakar daga zuciyata.
“Ba a banza
ba Bahaushe ya ce “ƙaramar
danga daɗin ƙetara.” Laifi ya
wuce na shuwagabanninmu da suka hana ruwa gudu? Nera goma sai ta gagari mutum –
sun zama ramin kura daga ke sai ‘ya’yanki. Ko laifi ya wuce na
malaman jami’o’i da suka sa komai ya ta’azzara?” Har kullum ba na so in riƙa tuna jami’a. Ba a banza ba ake mata laƙabi da “gidan ban kashi!” Zuciyata
ta sake dugunzuma yayin da na tuno da rayuwata ta baya, rayuwa gwanin ban sha’awa.
Duk wani nishaɗi da annashuwa suka yi ƙaura daga farfajiyar rayuwata. A yanzu babu abin da nake
so a duniya. Babu abin da yake burge ni.
Na fi so in kasance ni kaɗai.
Abubakar ya taɓa
tambaya na: “Shin ka san mene ne dangantakar ‘iska’ wato ‘aljani’ da ‘ɗan
iska’?” A lokacin ina sama, cikin zayon. Duniya tana ta lilo mai daɗi.
Ba na wani son magana. Sai kawai ya ci gaba da zuba: “Akwai kamanceceniya ne a
tsakaninsu. Sun yi tarayya a manyan ɓangarori
guda biyar, wato wurin zama da lokacin yawo da ɗabi’a
ko halayya da abinci da kuma kamanni. Ka ga misali, iskoki suna rayuwa a kangon
gidaje ko sakayayyen wuri mai datti. Haka ɗan
iska ma ke ɓoye kansa a ire-iren
waɗannan wurare domin aikata abin da ba ya so mutane su
gani... Haka kuma iskoki sukan yi yawo da dare a lokacin da ƙafa ta ɗauke. Shi ma ɗan iska
yakan yi haka domin ɓoye kaya ko harkar iskancinsa...”
Ya kalli murjin ƙato da ke faman
hayaƙi a hannuna sannan ya ci gaba: “Iskoki
suna cin ƙazanta da abubuwa da ka iya cutar da
lafiyar mutum. Shi ma ɗan iska ba baya ba ne a wannan fanni. A ɓangaren
halaye kuwa, ba sai na faɗa maka tarayyarsu ta fuskar ta’addanci ba. Da zarar
shaye-shaye ya yi wa mutum katutu, aikata ta’addanci da rashin mutunci abu ne
mai sauƙi a gare shi. A ɓangaren
kamanni kuwa...”
“Kana nufin ni ɗan
iska ne!” Na katse masa hanzari cikin fushi. Abubakar ya yi dariya sannan ya
ce: “Yo idan ma na ce hakan wani abu ne? Ko kai ba abokina ba ne? Babu irin
wasa ko zolaya da ba ma yi a tsakaninmu, kar ta san kar ne...” Na tari
numfashinsa: “Ka san dai ni ba wawa ba ne ballantana ka ce da wasa ake faɗa
wa wawa gaskiya.” Wannan ya faru kimanin makonni guda da suka gabata.
A yanzu kuwa, na kawo ƙarƙashin ƙatuwar bishiyar mangoro da nake zama. Wurin akwai sanyi
mai daɗi. Ƙananan
ciyayi suna gewaye da ita. “Fuck the world!” Na furta yayin da na zauna
cikin fushi sakamakon tunane-tunanen kayan haushi da suka dugunzuma zuciyata. Ban
ƙi a tashi duniya yau ba, kowa ma ya
mace! Abin da na fi saƙawa
ke nan a raina a cikin irin wannan yanayi. Na taɓa
jin wani malami yana cewa, wai: “Wanda ya ce ko sama da ƙasa za su haɗu... to ba shi da komai ne a tsakankaninsu.” Shi ma
haushi ya ba ni.
Na jawo baƙar ledar da ke aljihuna. Na kwance. Na fara watsa mai
da tsoho yaro guda huɗu. Daga nan na sanya wuta a bakin dula. Na yi
ajiyar zuciya bayan na yi zuƙar farko na
busa. Wata natsuwa ta fara lulluɓe ni. Duniya ta fara daɗi.
Me ya fi raina, wai cin tsiren mata? Tuni na ji gyangyaɗi
na famar ja na. Hausawa suka ce bacci ɓarawo. “Wannan
dai zance ne kawai.” Na raya a raina.
*** **** ***
Ban farga ba ashe hadari ya taso
gadan-gadan. Sararin samaniya ya murtuƙe
fuska. Aka fara kaɗa iska mai tsananin ƙarfi. Daga nan sai cida da walƙiya suka biyo baya. Kan ka ce kwabo an goce da ruwa kamar
da bakin ƙwarya. Na tashi na raɓe a
jikin bishiyar daidai wani babban reshe da ya mini rumfa.
Kai! Ruwan sama ikon Allah ne. A nan na
tuna labarin sarkin sauri da sarkin zilliya. “Ka ji zuge tamalle! Tsakanin ɗigaggan
nan za a ce mutum yana zillewa?” Daga nan kuma na tuno tarihin annabi
Nuhu (AS). “Da ruwa fa aka hallakar da jama’arsa... su kuwa Adawa da
iska. Amma ai waɗancan ruwa da iskar bala’i ne.”
Tunanin zucin ya fito fatar baki, duk don in ƙarfafa wa kaina guiwa yayin da tsoro ke ƙoƙarin mamaye
zuciyata.
Duk da haka na kasa hana zuciyata
tunane-tunane iri-iri. “To shin akwai tabbaci ne da ke nuna wannan ruwa da
iskar ba na bala’i ba ne? Ai da ma malamai sun ce a zamanin yau, muna aikata
dukkannin nau’ukan zunuban da kowace al’umma ta aikata a baya da har ya janyo
mata azabar Ubangiji!” Na raya a zuciya. “To ai ba na ɗaya
daga cikinsu.” Leɓɓana suka ba wa zuciyata amsa.
Daga nan wasuwasi ya ci gaba da mamaye
zuciyata tare da saƙe-saƙe iri-iri. Shi ya sa aka ce wargi ma wuri yake samu.
Lokaci ɗaya na ji tsoro ya mamaye ni. Nan na gane annabi ya
faku. “Ubangiji fa yana da hanyoyi da yawa na hallaka mutum.”
Tunanin zuci ne ya sake fitowa fili.
Nan kuma na tuna da cewa ba a son zama
a gindin bishiya musamman a jeji yayin da ake ruwa. An ce tsawa na iya sauka a
kan bishiyar. “Kai! Camfi ne kawai. Ita tsawar na da idanu ne da za ta gane
cewa wannan bishiya ce, kuma a jeji take?” Na sake faɗa
wa kaina domin samun ƙwarin guiwa. Can kuma sai na ce a zuciyata: “Kai!
Hanyar lafiya a bi ta da shekara.” Na kama hanya domin barin ƙarƙashin
bishiyar.
Ban gama fita daga ƙasanta ba aka yi wata walƙiya mai haske sosai. Daga nan tsawa mai ƙarfi ta biyo baya. Ina kallon wani abu mai kama da dunƙulen wuta ya yiwo ƙasa
tamkar an harbo kibiya. Kafin na yi wani motsi ya faɗo
daidai tsakiyar bishiyar. Nan take ta dare gida huɗu. Ƙarfin ƙarar da wutar
suka yi wurgi da ni. Feshin wutar ya watsu a jikina duk da ruwa da ake tsugawa.
Fuskata da tufafina suka yi baƙi ga ƙaurin hayaƙi tamkar na
shekara a maƙera. Buguwar da na yi a ƙasa da tsananin firgici tare da ƙarfin ƙarar su
suka sumar da ni nan take...
*** *** ***
“Likita, don Allah ka ji ƙaina, ka taimaka kada yaron nan ya mutu cikin wannan
hali.” Muryar mahaifiyata na ji. Har yanzu idanuwana a rufe
suke. Dukkannin gaɓoɓin jikina sun yi nauyi. Ba makawa a kan gadon asibiti
nake kwance. “Hajiya, kada ki damu. Ɗanki
zai samu lafiya da yardar Allah. Ku jira a waje. Ofisa raka ta waje.” Na san da
cewa yana nufin ofisan ya fitar da ita waje ne. Na yi ƙoƙarin buɗe
idanuwana, amma na kasa. Haka ma na kasa buɗe
baki domin magana.
“Yara sun ɓata
rayuwarsu kawai! Da me wannan ya yi kama? Wannan baƙin ruwa da kuke gani na fita daga bakinsa, dattin taba
sigari ce da sauran kayan shaye-shaye. Su ne ke taruwa a huhun mutum sannan su
gurɓata kayan cikinsa.” Muryar likitan na sake ji. Da alama
yana magana ne da waɗansu ma’aikatan asibiti. Kuma sai yanzu ne na ji lallai
wani ruwa mai wari na fita daga bakina.
Wani da ke gefe ya karɓi
zancen: “Ƙwayoyin maye ne fa iri-iri muka samu a
aljifansa, ciki har da tabar wiwi. In yaron nan ya mutu, lallai ya yi zuwan
zomo duniya. Na san Allah ne ya jefa masa wannan tsawa kansa domin ta zama darasi
da izina ga sauran mutane .”
Maganar ta girgiza ni. Na tsunduma
kogin tunani. “Wataƙila
maganar faɗuwar tsawa a jeji ba camfi ba ne. Allah
ne ke keɓance mutanen banza daga cikin gari ya
kai su jeji ƙarƙashin bishiya domin ya hallakar da su. Ai
Samudawa ma ta haka aka hallakar da su yayin da suka bijire wa dokokin
Ubangiji. Idan a cikin gari ne, abin zai shafi waɗansu.
Idan haka ne, lallai na shiga uku na lalace!” Hawaye
masu zafi suka biyo idanuwana da ke rufe. Nan kuma na ji na daina jin kowane
sautin murya, tamkar ina cikin wani wuri marar hayaniya ko kaɗan.
Sai kuma na ji zan iya buɗe idanuwa. Cikin gaggawa na buɗe
su.
Abin da na gani ya tsinkar mini da
zuciya. Wani ɗaki ne fari fat. Babu ƙofa ko taga a ciki. Babu kowa sai ni ɗaya.
Nan take kuma ya juya ya koma baƙi-baƙi ja-ja, gwanin ban tsoro. Kamar daga sama ko ƙasa sai na ga waɗansu halittu
masu tsananin ban firgici sun bayyana. Waɗansu baƙaƙe ne. Waɗansu
baƙi-baƙi da ja-ja. Waɗansu kuwa
jajir kamar garwashi, sannan tururin wuta na tashi daga jikinsu. Waɗansu
suna riƙe da gudumomi jajaye masu tururin wuta.
Ruwan wuta na narkewa tare da ɗiga daga jikin waɗansunsu. Na
firgita, na firgice. Na razana, na razane. Na tsorata, na tsorace. Na takura na
takure. Na shiga uku! Tabbas waɗannan mala’ikun azaba ne, kuma sun hasala, sun hasale.
Sun harzuƙa, sun harzuƙe. Sun dugunzuma, sun dugunzume. Sun fusata, sun fusace.
Sun tunzura sun tunzure. Na shiga uku! Kaicona!
Nan take zuciyata ta yi bulaguro zuwa
duniyar tunani. Na fara tuno dukkannin rayuwata ta baya. “Na san dai ina
sallolina duka. Sannan ba na cin haram. Amma kuma, ina laifi, amma guda ɗaya.
Shi ma ƙarami
ne. Shaye-shaye kawai nake yi.”
“Ƙarami?”
Wata kakkausar murya ta katse mini tunani. Ban san a sama ko ƙasa mai maganar yake ba. Muryar mai ban tsoro ta gauraye
wurin. Tamkar a cikin ƙoƙon kaina ake maganar. “Amma duk inda aka kawo maganar
bugarwa, to ana haɗawa ne da manyan zunubai kamar zina da cin alade da
makamantansu. Shin masu wa’azi ba su sanar da kai ba?”
Lamarin ya fi gaban a kwatanta shi da
firgici. Ko bayan yanayin ruɗani da katsewa da nake ciki, jikina a sassandare yake
yadda ba zan iya buɗe baki domin magana ba. To idan zan yi maganar ma me zan
ce? Zan amsa wa muryar da ta yi magana kan tunanin zuciyata ne?
Muryar ta ci gaba da magana: “Hikimar
mai yin halitta ne ya sa haramta shaye-shaye. Duk manyan laifuka da mutum zai
iya tunaninsu, to mai shaye-shaye zai iya aikata su. Wanda ke cikin maye, zai
iya zina, zai iya sata, zai iya kisan kai, zai iya aikata kowane nau’in
ta’addanci.”
Allah Sarki! Har na tuno da Abubakar.
Haka yake mini irin wannan huɗuba. Amma shi cikin kwanciyar hankali yake mini. Duk bayanin
da zan masa game da yadda harkar nan ke kwantar mini da hankali ba ya fahimta. Ƙarshe ma sai ya fara mini doguwar huɗuba:
“... abokina, ya kamata ka fahimta. Kana samun farin ciki ne daga shaye-shaye
saboda ka sa a ranka shi ne hanyar samun farin cikin naka. Misali, wanda ya ɗabi’antu
da ibada da karatun Kur’ani, karatu na kasancewa hanyar samun farin cikinsa.
Wanda ya ɗabi’antu da kallon finafinai, su ma sukan zama hanyar
samun farin cikinsa. Kai ne za ka koya wa zuciyarka... Kai ne za ka ɗora
ta a kan turbar da kake so ta saba da shi!”
A waccan rana sai da Abubakar ya zubar
da hawaye. Ya dube ni ya ce: “Lallai za ka ga na takura maka game da wannan ɗabi’a.
Amma abokina, ya kamata ka fahimci girman al’amarin. Za ka ji ayoyin Kur’ani da
dama sukan ƙare da tambayar cewa “Shin ba za ku
yi tuntuntuni ba?” Yanzu ka taɓa yin tunanin ɗimbin matsalolin da ke tattare da shaye-shaye? Ko kai a ƙalla za ka iya bayyana da dama daga ciki.”
Ya ja numfashi sannan ya ci gaba: “Ka
ga dai yana gurɓata ƙoda da
hanta da huhu da waɗansu kayan cikin mutum. Shi ya sa a jikin kwalin taba
sigari aka rubuta ɓoro-ɓoro cewa, MASU SHAN SIGARI NA IYA MUTUWA DA WURI. Lallai
kuwa ɓera ma ya fi mai shaye-shaye basira, domin da ya san an ɗana
tarko, da ba za ya kai bakinsa kan abincin da aka sanya ciki ba. Ko bayan nan
ga sanya mutuwar zuciya da gushewar tunani mai kyau. Kana ganin yadda ‘yan
shaye-shaye ke komawa ɓarayi saboda lalacewa.” Lallai Abubakar ya kasance mai
wasiyya da haƙuri
kuma “bil hikimati.”
Ya fuskance ni cikin alamun jaddadawa.
Ya fara da tambaya: “Ka san wani abu?” Bai jira amsata ba sai ya ci gaba da cewa:
“A Arewacin Nijeriya, kusan kashi hamsin na majinyatan da ke asibitocin masu taɓin
hankali wato psychiatric, shaye-shaye ne ya kai su!”
“Za ka mutu kana ƙasƙantacce, a
matsayin wanda ya kashe kansa!” Kakkausar muryar nan ce ta tsamo ni daga kogin
tunanin da na tsunduma. Muryar ta ci gaba: “Da
ma kullum sai ka yi ƙoƙarin kashe kanka ta hanyar jefa rayuwarka haɗari
bisa sani.” Daga nan sai na ji wata tsawa marar misaltuwa. Dukkannin jijiyoyin
jikina sai da suka tsittsinke. Numfashina ya daina ƙarasawa cikin cikina.
Na shiga cikin da na sani mai tsanani. “Kaicona!
Lallai na yi wasa da damarmakina. Ina ma a ce mafarki nake yi, ko kuma idan da
gaske ne ma Allah ya jinkirta mini kaɗan...
Lallai da zan zama mai aikata aikin alkairi, sama da kowa a duniya.” Tamkar
muryar nan ta ji ni, sai na ji an ce: “Shin ba ai ta ba ka damarmaki a baya ba?
Shin ba a yi ta maka wa’azi ba? Lallai ba ka gaskata maganar Ubangiji ba da ya
ce kamunSa na da tsanani! Sannan Allah ba ya jinkirta wa wata rai idan
ajalinta ya zo!”
Haƙiƙa fitar rai
bala’i ne, azaba ne!
*** *** ***
Da
aka shigo da ni cikin maƙabarta
ne hankalina ya ƙara
tashi. Ƙarar da ta
fito daga cikin wani kabari da ke nan gefe ta sa tsuntsayen da ke wata bishiya
suka firka cikin firgici. Mutanen da ke tare da ni ba su ji ƙarar ba, haƙiƙa da
sun ji, da sun yasar da ni sun juya a guje, ko kuma su suma domin firgici. Ko
na yi musu ishara na san aikin banza ne domin ba sa jin maganata. Yanzu kam na
gane kabarin da ƙarar
ke fitowa. Gwamnanmu ne da ya rasu kimanin sati uku da suka gabata.
Aka
ƙara
maimaita wannan ƙara.
Daga nan sai na ji wata kakkausar murya na tuhumar sa: “Shin wa’azi bai iso maka ba game da haƙƙoƙin
shugabanci? Shin ba ka yarda da Ƙur’ani da Hadisai ba ne inda Ubangijinka ya ce zai kama ka
kamu mai tsanani idan ka ƙi
sauƙe nauyin da
ke kanka? Shin Ubangiji bai kasance mai gaskiya ba ne cikin alƙawuransa? Ba ka yi komai ba domin
dakatar da safarar ƙwayoyi.
A maimakon haka, kun goyi bayan shaye-shaye domin samun ‘yan bangar siyasa da
za su kare muradunku. Kun goyi bayan safarar ƙwayoyi domin al’umma ta daɗa
lalacewa sannan a samu yawaitar zaman banza, wanda hakan ne zai ba ku damar ci
gaba da shimfiɗa zalunci da juya talakawa. Kun ƙi bin matakan hana safarar kayan maye
domin ku samu maƙamin
da za ku yi amfani da shi wajen gurɓata
tunanin matasa don cimma muradunku.” Muryar ta ƙara tsiwa da kaushi: “Wannan shi ne sakamakon zalunci da son kai! Za ka ɗanɗani
azaba kafin ranar ƙiyama
inda za ka riski sakamakonka!” Ihu ya sake biyo baya. Da na lura, sai na ga
kabarin ya yi jawur, sannan har girgiza yake yi saboda bala’i. Na ƙara shiga cikin tashin hankali!
Wani
wari da tiriri mai zafi ya ja hankalina. Da na lura sai na ga suna fitowa ne
daga wani kabari da ke nan gefe. Lallai kuwa na gane kabarin. Na Alhaji Mai
Dula ne. Ana masa laƙabi
da Mai Dula saboda ƙaurin
suna da ya yi wajen safarar kayan maye. Sau da dama ‘yan sanda ko jami’an
yaƙi da
safarar miyagun ƙwayoyi
na kama shi. Amma duk lokacin da aka kama shi, za ka ji al’umma na cewa: “Aikin
banza! Duk dodo ɗaya suke yi wa tsafi.” Kuma lallai
aikin banzan ne yi wa kare wanka, domin ba ya daɗewa
ake sako shi. Shi da kansa yakan ce: “Wace rana ce jemage bai gani ba?”
Daga
ƙarshe an ce
rajista ya yi da waɗansu jami’ai. Duk lokacin da ya yi badaƙalarsa, to sai ya kai musu cin hanci.
Saboda haka, ba sa baza homarsu ta wurin da yake. Sun zama kar ta san kar
wai ɗan kanoma ya san munta.
Da
muka yi kusa da kabarin, sai na ji wata murya mai ban firgici na cewa: “A
dalilinka ne tarbiyyar mutane da dama ta gurɓata.
A dalilinka ne mutane da dama suka rasa rayuwakansu sakamakon shaye-shaye. A
dalilinka ne aka aikata miyagun ayyuka daban-daban bayan an bugu. Ka ɓata
kuma ka ɓatar. Da kana tunanin mutuwa ƙarya ce? Alƙawarin Ubangijinka ne ba ka yarda da
shi ba ko azabarSa? Za ka ci gaba da ɗanɗana
uƙuba kana ƙasƙantacce!”
Muna
matsawa gaba abin da na gani ya sake firgita ni. Kabarin wani babban jami’in ɗamara
ne. Bai fi wata guda da rasuwa ba. Na kuwa gane muryarsa. Yana ta kururuwa babu
ƙaƙƙautawa. Ina kallon waɗansu
ƙattin baƙaƙen
macizai suna shige da fice cikin kabarin ta ɗan
wani wuri da ya yi rami. Sannan kabarin yana ta tururin zafi. Nan kuma na jiwo
makamanciyar muryar nan kakkausa tana cewa: “Kana da damar yaƙi da shaye-shaye sannan nauyi ne da ya
rataya a wuyanka, amma ka biye wa son zuciya da son duniya. Kai ka taimaka wa
masu safarar kayan maye domin abin duniya da kake samu. Wannan kaɗan
ke nan daga uƙubar
da ke dakon ka a madakata.”
Kusa
da shi kuwa wani kabari ne wanda shi ma ana ta kururuwa a ciki. Tururi da hayaƙi na fitowa daga cikinsa. Na ji wannan
murya na cewa: “Kai ka nemi matsayi a jami’a, Ubangiji kuma Ya ba ka. Da
saninku ake danne haƙƙoƙin ɗalibai
a jami’a. Da saninku ake sanya rayuwarsu cikin ƙunci. Ɗalibai da dama sun bar karatu saboda
halin ƙunci da
kuka jefa su. Kun jefa ɗalibai da dama kan turbar laifukan da
suka kai an kore su daga makaranta. Ku ne silan taɓarɓarewar
tarbiyyarsu. Ku ne silan rugujewar rayuwarsu. Ku ne silarsu ta kama zaman banza
da shaye-shaye. Za ka ɗanɗani
ƙunci kamar
yadda ka ƙuntata wa
al’ummar Annabi!”
Yanzu
kam na fara hango kabarin da aka tona mini. Na ƙara shiga cikin firgici marar
misaltuwa. Wuta ce na hango mai tsananin tsiri da balbaluwa tana ci a ciki. Waɗansu
ƙattin
macizai da baƙaƙen kunamu suna ta faman safa da marwa a
ciki. Na fara ihu da kururuwa. Na fara musu magiya da kada su kai ni wannan
wuri. Amma ba sa ji na, kuma babu wanda ke kallon wannan bala’i. Na ƙara shiga cikin damuwa mai tsanani tare
da da na sani mara misaltuwa.
Aka
ajiye makarar da nake ciki kusa da wani kabari. Na kuwa shaida kabarin na Malam
Audu ne. A wurin ɗansa nake sayen wiwi wani lokaci. Na
jiyo shi a ciki yana ihu irin na wanda ke cikin matsananciyar azaba. Muryar nan
kuwa da na saba ji tana cewa: “Ka haihu kuma ka ƙi ba wa ‘ya’yan tarbiyya! Kai ne silan da ya sa
suka taso a matsayin sagartattu. Rashin kulawarka ta sa suka hau turbar
shaye-shaye. Shin saƙo
bai iso maka ba cewa ku kare kanku da iyalanku daga shiga wuta ba? To
taka ta same ka!...”
“A gabato da shi.” Wani malami ya faɗa
yayin da aka kammala kimtsa ramin da za a
saka ni. Na ci gaba da kururuwa marar amfani yayin da na ga an doshi
wannan balbalin bala’i da ni. Tun daga nesa tiririn da ke fita a ciki yake bugu
na. Ko kaɗan babu mai kallon abin da ke faruwa, kuma babu wanda
yake ji...
Na yi nadama mai tsanani game da yadda
na banzantar da rayuwata. Na shiga da na sani bi da bi. Da a ce zan koma
duniya, lallai duk yadda aka ɓata mini rai, to haƙiƙa ba zan jefa kaina a shaye-shaye ba. Da zan yi rayuwa
irin yadda Bahaushe ke cewa, in dama ta ƙiya
a koma hagu. Da zan koma duniya, da na yi wa’azi ga abokaina da sauran matasa
da na sani cewa, duk rintsi su daina zaman banza. Lallai zuciyar mai zaman
banza fadar sheɗan ce. Dama ake ba wa sheɗan
domin ya yi ta ingiza mutum zuwa gurɓatacciyar
turba.
Da a ce zan koma duniya, da na faɗa
wa malaman addini cewa dole su sauya salon wa’azi game da illolin shaye-shaye. Da na ba da
shawarar hukumomi su haɗa kai da malaman kiwon lafiya da jami’an kiwon lafiya da
malaman makaranta da shuwagabannin
gargajiya domin ganin an shawo kan matsalar shaye-shaye. Da na ba da
shawarar a samar da wani shiri da zai sa kowane ɗan ƙasa ya zama jami’in yaƙi da shaye-shaye ta hanyar faɗakarwa
da ba da rahoto ga hukumomi da suka kamata.
Aka matsa da makarar bakin ramin da ke
cike da bala’i da azaba. Na ci gaba da kurma ihu ina cewa: “Allah na tuba! Na
yi alƙawarin gyara halayena. Na yi alƙawarin hanuwa daga dukkannin abubuwan da Ka haramta. Na
shaida azabarKa gaskiya ce. Na shaida mutuwa gaskiya ce...”
Tun kafin a sanya ni cikin ramin, sai
waɗansu ƙattin murtuƙa-murtuƙan baƙaƙen macizai
biyu suka yo tsalle daga ciki suka cafke hannayena. Ɗaya ya riƙe hannun
dama, ɗayan kuma ya riƙe
na hagu. Na ƙara kurma ihu tun kafin in ji zafin
cizon nasu. Amma sai ban ji zafin ba. A maimakon haka, sai na ga macizan sun kamo
hannayen mutane. A gefe guda kuwa na ji ana cewa: “Subhanallah! Innalillahi wa
inna ilaihi raji’un. Mafarki ne yake yi ko ya zautu ne?”
Firgigi na buɗe
idanuwana. Ashe gaskiyar Bahaushe da ya ce bacci ɓarawo
ne – sannan zai iya sace kowa. Ni da nake son komawa gida bakin magariba, na
kwana har na hantse a jeji. Na haɗa gumi sharkaf.
Na ɗaga
ido na dubi manoman guda biyu da suka zuba mini na mujiya. Duk cikinsu babu
wanda ya san ni. Ɗaya daga
ciki ya ka da baki ya ce: “Saurayi in ce ko lafiya?” Na buɗe
baki da niyyar amsa musu. Ashe ihun da na yi ta yi ya dusashe mini murya. Kawai
sai na gyaɗa musu kai sannan na yi yaƙe. Su biyun suka haɗa baki: “To
Allah ya sauwaƙe.”
Daga nan suka kama gabansu.
Na yi shiru ina bitar dukkannin
abubuwan da na gani a mafarki. Ban san lokacin da na yi sujadar godiya ga
Ubangiji ba. Na miƙe nufi gida
cikin gudu-gudu sauri-sauri. Ina tafe ina saƙe-saƙe iri-iri. “Idan
da na mutu da gaske fa da na taɓe taɓewa,
da na lalace lalacewa, da na halaka halakewa!” Ban san lokacin
da na fara zubar da hawaye ba, ko dai na tsoro, ko na da na sani, ko kuma na
murna da farin cikin samun DAMAR TUBA.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.