Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsattsafin Fandare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Wakokin Baka na Hausa

Cite This Article: Bakura, A.R. & Sani, A-U.  (2023). Tsattsafin fanɗare wa addinin Musulunci: Wata yasasshiyar gona a gandun waƙoƙin baka na Hausa. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, (6)10, 482-489. https://doi.org/10.36349/easjehl.2023.v06i10.002.

 Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

Adamu Rabi’u BAKURA
Department of Languages and Cultures,
Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria
E-mail: adamubakura@fugusau.edu.ng,  arbakura62@gmail.com

&

Abu-Ubaida SANI
Department of Languages and Cultures,
Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria
E-mail: abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng, abuubaidasani5@gmail.com 

Tsakure

Rubuce-rubucen nazari da aka yi game da waƙoƙin Hausa sun fi shurin masaƙi. Duk da haka, mafi yawan rubuce-rubucen sun karkata ne kan zaƙulo fasahohi da ke cikin waƙoƙin tare da nuna yadda suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Wannan takarda na da fahimtar cewa an bar wani babban giɓi wanda shi ne nazarin fanɗare wa dokokin addini cikin waƙoƙin Hausa. Maƙalar nan na da manufar binciko muhallan da ɗiyan waƙoƙin baka na Hausa suka keta dokokin da Allah ya shimfiɗa wa bayinsa. An tattara bayanai ta hanyar sauraron waƙoƙin da tsamo misalan ɗiyan waƙoƙin da abin ya shafa, tare da ciro hukunce-hukuncen da suka yi bayani kansu daga Alƙur’ani da hadisan manzon Allah. Binciken ya fahimci cewa, akwai tarin misalan fanɗare wa addini a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Daga ƙarshe an ba da shawarwarin da suka haɗa da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da ire-iren waƙoƙin ba su yi tasiri wajen gurɓata tarbiya nagartacciya ba.

Fitilun Kalmomi: Waƙoƙi, Addini, Musulunci, Fanɗarewa

1.0 Gabatarwa

Musulmi ba a bar shi kara zube ba. An kafa masa sharuɗɗan tafiyar da rayuwa dukkanta. Ire-iren waɗannan sharuɗɗan suna ƙunshe cikin littafin Allah (Alƙur’ani) da Hadisan Annabi S.A.W. Daga cikin dokokin akwai na tilas, wato abin da Musulmi mai hankali ba zai iya rabuwa da shi ba, komai tsanani. Akwai kuma abubuwan ƙi, wato waɗanda ba a so Musulmin ya aiwatar da su ba. Haka akwai haramun, waɗanda aka hana mutun ya aikata su. Idan dukkannin rayuwar mutum ta kasance cikin ɗa’a, kuma ya nisanci saɓo, babu shakka ya kiyaye dokokin Allah Maɗaukakin Sarki.

A gefe guda kuwa, kamar yadda Chiromawa, (n.d. p. 5-10) ya bayyana, ko da addinin Musulunci ya iso ƙasar Hausa,[1] ya tarar da al’ummomi da dama suna aiwatar da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe nau’i-nau’i da suka haɗa da:

i.              Kiɗan sana’a

ii.            Kiɗan jawo hankali

iii.         Kiɗan lallashi (rarrashi)

iv.         Kiɗan faɗakarwa

v.            Kiɗan zaburarwa

vi.         Kiɗan ƙarfafa zuciya

vii.       Kiɗan jaruntaka

viii.     Kiɗan farin ciki

ix.          Kiɗan ibada

Duk ire-iren waɗannan kaɗe-kaɗe akan haɗa su ne da waƙe-waƙe. Kasancewar addinin Musulunci, addini ne mai sauƙi da sauƙaƙa wa mabiyansa, bai haramta waɗansu daga cikin nau’ukan kaɗe-kaɗe ba. Ya dai kawo gyare-gyare domin kare mutunci da martabar mabiyansa. Ya haramta shi ne yayin da aka aiwatar da abin da Allah ya haramta a cikinsa.[2] Hasali ma akwai wuraren da Musulunci ya sunnanta kiɗa da waƙa, kamar a lokuttan ɗaura aure, tamkar yadda Imamu Buhari ya bayyana a “Babin Kaɗa Ganha” a ranar aure da walima. Bayan haka, akwai ranar kai amarya ɗakin mijinta, da ranar idi da ranar suna, da ranar zuwan wani shugaba da ranar komawarsa, da ranar kaciya (kugunu/kuidu). Akwai hadisai waɗanda Buhari da Muslim da Tirmizi da Hakimu da Nisa’i suka rawaito da ke nuni ga halaccin kiɗa da waƙa a babin aure da sallar idi. Halaccin kan tabbata ne matuƙar bai haɗa da alfasha ko motsawa zuwa ga saɓon Allah ba.

A bisa wannan ne, maƙalar ta ƙuduri aniyar yin ƙwarya-ƙwaryar bincike a muhallan da makaɗan baka na Hausa suka keta ƙa’idojin da Allah ya shata ta hanyar kauce musu. Duk wasu ɗiyan waƙa da makaɗi ya yi za a yi ƙoƙarin kawo shi tare da auna shi da ma’aunin shari’a da aka ciro daga nassin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. domin tabbatar da hasashen. Ana iya samun ɗiyan waƙoƙin da ke ƙunshe da gurbin fanɗara a waƙoƙin makaɗan sarauta, da na jama’a da na maza da sauransu, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.

1.1 Dabarun Gudanar da Bincike

Kadadar wannan bincike ta taƙaita ne ga waƙoƙin baka na Hausa a farfajiyar koyarwar addinin Musulunci. A ɓangaren waƙoƙin an ɗauko ɗiyan waƙoƙi da aka tattauna kansu kai tsaye ta hanyar sauraron odiyo-odiyo da kallon bidiyoyinsu. A ɓangaren hukunce-hukuncen addinin Musulunci kuwa, an ɗauko su kai tsaye daga cikin Alƙur’ani mai tsarki da hadisan Manzon Allah (S.A.W.) ingantattu. An kuma nazarci rubuce-rubucen masana da manazarta a wannan fannin inda suka haska hanya ga binciken.

2.1 Fanɗare wa Koyarwar Musulunci ta Hanyar Zambo

Makaɗan saurauta sun shahara wajen yin zambo, domin ƙawata waƙoƙinsu. Masana da dama sun bayyana ma’anar zambo gwargwadon fahimtarsu. Gusau, (1984 p. 37) ya tafi kan cewa “Akan yi zambo don adanta waƙa da muzanta wanda ke hamayya da wanda ake yi wa waƙa.Abba da Zulyadaini, (2000 p. 63) sun bayyana zambo da cewa: “... nau’i ne na muzanta mutum ta hanyar ƙasƙantar da shi, ko wulaƙanta shi, domin a baƙanta masa tare da dusashe masa kwarjini a idon jama’a. Mawaƙan sun fi shahara da zambo don su aibanta duk wani ɗan sarki da ke ja da ubangidansu.  Muhammad, (2005) kuwa na da ra’ayin cewa zambo zagi ne kai tsaye,

... saboda akan ba da hoton wanda ake yi wa tare da bayyana cikakkiyar sifarsa ta hanyar ambaton duk wani abu da ya dace da shi. A lokacin da aka yi ma wani zambo akan fito da hotonsa ne zahiri, ta yadda duk wanda ya san shi zai gane cewa da shi ake. Muhammad, (2005 p. 28)

A taƙaice ke nan, zambo yana ƙunshe da ma’anar ƙaga wa mutun magana wadda za ta muzanta shi ta ɓata masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba. A dubi misalin zambon da Alhaji Musa Ɗankwairo ya yi wa wani ɗan sarautar Tsafe:

Kun san zamanin ga ya canza,

Ga wani ɗan sarki da kandaye,

Ya shaho hoda kamar Delu.

(Ɗankwairo: Waƙar Sarkin Tsahe).

Wannan zambon da Ɗankwairo ya yi wa ɗan sarki ya kai matuƙa wajen aibanta ɗan sarkin ta hanyar kamanta shi da ɗan daudu. Hakan ba ƙaramin muzantawa da dushe masa kima ya yi a idon al’umma ba. Tabbas kuwa hakan ya saɓa wa dokokin addinin Musulunci. An umurci Musulmi da ya tsare (kame) harshensa da yin furucin abin da bai halatta ba, kamar keta mutuncin ɗan uwansa Musulmi ba tare da wani abu mai wajabtawa ba na shari’a. Allah na cewa:

Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa, da ba wa ma’abocin zumunta kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana yi muku gargaɗi ko da kuna tunawa. (Surar Nahli: 16:90).

Idan aka dubi wannan ayar za a tarar ta yi hani ga yi wa wani mugun baki (mugun fata), sannan ta yi hadi ga alfasha. Ya kuma yi umurni da tausayawa tare da yin abu bisa gaskiya. Daga ƙarshe ta yi hani a kan ha’intar wani ta kowane ɓangare. Wannan na iya kasancewa ta hanyar lafazi ko a aikace. Ta la’akari da wannan ɗiyar waƙar, za a tarar mawaƙin ya kauce wa dokar da Allah ya ɗora masa.

Annabi S.A.W. ya ce:

Haƙiƙa, mafi sharrin mutane a matsayi wurin Allah a ranar alƙiyama shi ne wanda mutane suka ƙyale shi don ƙiyayyar alfasharsa. (Muslim ya ruwaito).

Wanda duk wani mawaƙi ya yi wa zambo, to zai guje shi tare da yin kaffa-kaffa da al’amarinsa. Sau da yawa akan ba su kyauta ne bisa tilas don gudun zambonsu. A irin wannan yanayin idan aka nazarci hadisin, za a ga a nan ma sun kauce wa koyarwar Annabi S.A.W.

A wani Hadisin kuwa Annabi (SAW) cewa ya yi: “Mumini bai kasancewa mai yawan suka ba ko yawan la’anta ko yawan alfasha, ko mai sakin harshe” (Tirmizi ne ya ruwaito shi). Wannan hadisin ya fito ƙarara ya bayyana mana cewa, duk mawaƙin da ya ba da gaskiya ga Allah da ranar lahira da manzancin Annabi S.A.W., zai kasance mai bin dokokin Musulunci kamar yadda suke. Hakan kuwa zai sanya ya guji yi wa Musulmi zambo.

Akwai misalan wuraren da makaɗan jama’a suka yi wa abokan hamayyarsu zambo ta hanyar zagi kai tsaye. A irin wannan lamari ne mawaƙin jama’a kan fito da halayen mutun a fili, sannan ya zage shi. Misali, a waƙar “Gagara Badau,” Alhaji Mamman Shata cewa ya yi:

Shata: Allah ya tsine ma tsohon mazinaci,

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

 

Shata: Allah ya tsine ma da kai da iyalinka.

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

.....

Shata: Yanzu babban ɗan bai gani,

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

 

Shata: Babban jikanshi kuma yana kama agwaginmu,

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

 

Shata: Gida ya lalace.

Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

Dubi yadda Shata yake zagin wani basarake tare da nuna ɗansa ya makance, ya kuma kira jikansa ɓarawon agwagi. Wannan ba ƙaramar fanɗarewa ba ce, domin a shara’ar Musulunci an umurci Musulmi da ya kiyaye da yin zance da bai halatta ba, kamar ƙarya, da zage-zage da keta mutunci Musulmi. Allah na cewa: “... Kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana muku gargaɗi ko da kuna tunatuwa.” (Alƙur’ani, Suratul Nahl, 16:90).

2.2 Fanɗare wa Koyarwar Musulunci ta Hanyar Habaici

Habaici ko gugar zana salo ne ko azancin yi da wani a kaikaice ta yadda sai wanda ya san shi kuma ya san abin da ake magana game da shi ne kaɗai zai iya ganewa. Habaici wata hanya ce da makaɗan baka suke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin ƙara musu armashi, ta hanyar ƙasƙantar da wani mutun ko kuma muzanta shi ko su zage shi ko kuma su soka masa wata magana a kaikaice. Misali, a cikin waƙar Mai Dubun Nasara Sardauna, Alhaji Musa Ɗankwairo yana cewa:

Ga kare ga kura kowane ya hangi wani,

Ga aura ya koma,

Wagga nan hanya ba mu ga wurin wali ba.

(Alhaji Musa Ɗankwairo, Waƙar Mai Dubun Nasara, ta Sardauna).

Yayin da aka dubi ɗiyar wannan waƙar za a ga yadda Ɗankwairo ya siffanta Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da kura. Ya yi hakan ne domin bayyana irin ƙarfinsa kamar yadda kura ke da shi. Wannan kuwa ya shafi yadda take iya tauna ƙashi da kuma kwarjini da waibuwarta na sanya rashin kuzari ga halittar da ta tunkare ta. A gefe guda kuwa, sai ya kira wanda yake yi wa habaici da kare, saboda ba sa zama inuwa ɗaya da kura. Hasali ma kare ba ya hangen nesa sosai, kuma mai gidansa yakan yi amfani da shi ne wajen farauta. Kiran mutun kare ba ƙaramin ƙasƙantarwa ba ne a al’adance. Wannan ne ya sa makaɗan baka sukan siffanta waɗanda suke son wulaƙantawa da kare saboda halayyarsa da ɗabi’unsa.

Musulunci ya hana keta mutuncin Musulmi ko wulaƙanta shi ko zagin sa ko laƙa masa munanan sunaye, ba tare da haƙƙin shara’a ba. Allah na cewa: “… kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye(Alƙur’ani, 49:11).

Idan muka dubi wannan ayar, za mu ga cewa ta hana a kira Musulmi da sunan da zai kasance tamkar zagi ne gare shi. Yin haka kuma fanɗare wa umurnin Ubangiji ne. Annabi S.A.W. ya ce: “Zagin Musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙar sa kafirci ne” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

Idan aka dubi wannan hadisin cikinsa da wajensa, aka kuma nazarci ɗiyar waƙar da ta gabata, za a tarar cewa, makaɗin ya kauce wa faɗar Annabin S.A.W., ya yi gaban kansa. Yin haka fanɗarewa ne ga dokokin addinin Musulunci. Bin dokoki da ƙa’idojin Musulunci kuwa dole ne, inda har Allah ke cewa: “Kuma abin da Manzo ya zo muku da shi, to ku riƙe shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu” (Surah Al-hashr, 59:9).

3.0 Fito-na-Fito da Koyarwar Muslunci

Akwai misalan inda mawaƙa ke amfani da wasu kalmomin da suka kauce wa ƙa’idojin addinin Musulunci. Akan samu irin wannan fito-na-fito a fannonin da suka shafi sahihan aƙidojin da suka danganci ranar lahira, da matsayin mala’ikun Allah da makamantansu. Ya kuma haɗa da dokoki da ƙa’idojin addinin Musulunci ta fuskar hani da horo. Wannan bangare na aikin zai mayar da hankali wajen zaƙule ire-iren waɗannan misalai:

3.1 Izgilanci

Izgilanci ga abubuwan da addini ya zo da su na nuni ga halin ko-oho ga lamarin addinin. Musulunci kansa ya tsawatar da riƙo da dokokin da ke ƙunshe cikinsa ba tare da wargi (wasa) ba. Duk da haka, akan samu wuraren da mawaƙa suka yi izgilanci ga lamarin addini. Alhaji Muhammadu Ɗan’anace a waƙar Shago yana cewa:

Jagora: In da lahira ana kasa dambe...

‘Y/Amsohi: Da Walakiri ya ji ƙwal ga gaba nai.

......

Jagora: Duk wanda bai yi kallon Shago ba,

Aradu yana da sauran kallo,

Ya zaka duniya kamar bai zo ba,

Kamar zuwan kare ga aboki,

Tamkar mutum ya mari budurwa,

Ko ya mutu ba a gafarta mai.

In aka dubi wannan ɗan waƙar, za a tarar cewa, wannan makaɗin ba ƙaramar kasada ya yi ba. Ya nuna rashin jin tsoron aukawar wani haɗari (hatsari) ko shiga cikin abin da bai san sakamakonsa ba. Allah na cewa: “Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi a kansa.” (Surar Isra’i, 17:36).

Idan muka nazarci wannan ayar, za a ga yadda Mahaliccin sammai da ƙassai ya faɗakar da masu imani da su yi kaffa-kaffa ga dukkan lamarin da ba su san haƙiƙanin yadda yake ba. Ko bayan batu kan abin da mutum bai sani ba, batutuwan da ke ƙunshe cikin ɗiyar waƙar na tattare da izgilanci ga abin da ya shafi imani da mala’iku da ranar ƙiyama.

3.2 Goyon Bayan Karuwanci

Kalmar karuwa, suna ne na mace. Jam’i kuwa shi ne karuwai. Karuwa na nufin mace mai zaman kanta wadda mazan banza ke neman ta su ba ta kuɗi domin saduwa (zina) da ita. Zina kuwa tana nufin saduwa (jima’i) da matar da ba ta halatta ga mutun ba ta hanyar aure, wato wadda ba matarsa ba.

Tun kafin bayyanar Musulunci a farfajiyar ƙasar Hausa, Bahaushe ya ƙyamanci zina. Don haka karuwanci bai samu bagiren zama ba, balle a yi zina. Duk da kasancewar akwai al’adar tsarance, a inda saurayi kan gayyaci budurwarsa ta je ɗakinsa har ma ta kwana. Sakamakon irin wannan al’adar ce, ya sanya su amfani da al’adun tsafi domin tabbatar da amarya ba ta taɓa sanin wani ɗa namiji ba (zina) kafin a yi mata aure. A irin wannan al’adar ce, idan yarinya ta san maza kafin a yi mata aure, za ta kunyata a cikin jama’a. Idan kuma ta ɓoye ba ta faɗa ba, ta mutu, kamar yadda Ibrahim, (1985 p. 5) ya nuna.

Yayin da addinin Musulunci ya bayyana, sai ya haramta zina. Hasali ma ya sanya ta cikin manyan laifuka, bayan kafirci, wato haɗa Allah da wani da kashe ɗan Adam. Allah yana cewa: “Kuma kada ku kusanci zina, lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Alƙur’ani; Suratul Isra’i, 17:32).[3]

Haka kuma Musulunci ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da za ta iya zama sanadin aikata zina ta hanyar wajabta wa mata sanya hijabi. Sanya hukuncin jefe mazinaci da mazinaciya har su mutu a bainar jama’a, idan sun yi aure, ko a yi musu bulala idan ba su taɓa yin aure ba, na nuni da girman zunubin.[4]

Duk da wannan umarni na Ubangijin talikai da kuma uƙubar da aka tanadar wa mazinata, sai aka sami wani mawaƙi da ake kira Habibu Sakarci ya yi wa wata karuwa waƙa. A cikin ɗiyan waƙar yana cewa:

Jagora: Shehuwar mata Safiya Kano,

Ta gidan ‘Yajja Safiya Kano.

 

Jagora: ‘Yan birni roƙo suke,

Allah ba mu jaka bakwai,

Mu gano ɗakin Safiya Kano.

 

Jagora: Direbobi ma roƙo suke,

Allah ba mu jaka bakwai,

Mu gano ɗakin Safiya Kano.

 

Jagora: Mutan birni yanga suke,

Domin darajar Safiya Kano.

Yayin da aka nazarci ɗiyan waƙar, za a ga cewa Habibu Sakarci yana tallar wannan karuwa ta hanyar bayyana ta a matsayin ƙasaitacciyar karuwa. Har ma ya nuna ‘yan birni da dirobobi na burin Allah ya ba su kuɗi masu yawa, don su tafi ɗakinta. Hasali ma ya bayyana ta fi sauran karuwan birnin kyau. Wannan ba ƙaramar fanɗara ba ce da keta dokokin Allah. Ya zo cikin hadisi Annabi S.A.W. yana cewa:

Lalle ana rubuta wa ɗan’adam rabonsa daga zina, kuma lalle mai risker sa wancananka ne babu makawa. Idanu zinarsu ita ce kallo, kunnuwa kuwa zinarsu ita ce sauraro, harshe kuwa zinarsa ita ce zance. Hannuwa kuma zinarsu ita ce damƙa, ƙafa kuma zinarta ita ce taku, zuciya kuwa saƙa soye-soyenta ne, kuma tana guranta su, farji yana gaskata wancananka ko ya ƙaryata (Buhari da Muslimu ne suka ruwaito hadisin).

Duk da irin waɗannan nassoshin Alƙur’ani da hadisan Annabi S.A.W., sai ga ya makaɗa na fanɗare musu ta hanyar gayyatar al’umma zuwa ga aikata fasiƙanci. Shi ma Alhaji Mamman Shata ya yi makamanciyar wannan waƙar, a inda ya yi wa wata mata da ake kira Karo Oma:

Jagora: Duk ɗan birnin da ya riƙa,

Ni kar ya yi mini yanga,

In yana so ya isa

In gan shi gidan Kara Oma.

(Alhaji Dakta Mamman Shata: Waƙar Kara Oma)

A nan Shata ya fito ƙarara ya tura ‘yan birni su tafi gidan wannan karuwa idan har sun isa. A ɗaya ɓangaren kuwa cicciɓa ta ya yi da cewa, sai manyan mutane wayayyu ne kawai suka isa su yi hulɗa da ita. Wannan waƙar ba abin da ya raba ta da fanɗare wa dokokin Allah da ya shata wa Musulmi.

A shara’ar Musulunci, an san Musulmi da kunya. Hasali ma kunya tana cikin halayensa, kuma tana daga cikin Imani.[5] Imani kuwa shi ne aƙida da rayuwar Musulmi. Manzon Allah yana cewa: “Kunya da imani suna zozozo da juna. Idan babu ɗayansu, ɗayan ma ba za a same shi ba” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

3.3 Goyon Bayan Shan Giya

Giya, kalmar suna ce da ke cikin jerin sunaye jinsin mata. Ita kuma nau’i ce da ake yi da hatsi ko alkama ko inibi wadda ake sha a yi maye. Ana kuma kiranta barasa., kamar yadda ƙamusan CNHN (2006 p. 168) ya nuna.

Shan giya a tsakanin al’ummar Larabawa kafin bayyanar Musulunci abu ne sananne. Shi ne ƙashin bayan doron ginin tattalin arzikinsu, kuma giya na daga cikin kayan fataucinsu. Har matansu sun kasance shahararru wajen haɗa ta. Hasali ma kowane gida akan same ta. Wannan ya sa har suna yabon giya a cikin waƙoƙinsu.

Su ma al’ummar Hausawa ba a bar su a baya ba, domin sun mayar da shan giya musamman a lokuttan bukukuwan aure da na haihuwa tamkar ƙawa. Yayin da suka samu rabauta na karɓar addinin Musulunci, sai suka guje ta a sakamakon hanin da addinin ya yi gare su.

Kasancewar Musulunci addini ne mai sauƙi da ke ƙunshe da dabarun magance abubuwan da ke haifar da fitsara da ta’addanci a tsakanin al’umma, sai ya fara bayyana wa muminai rashin kyanta.[6] Daga nan kuma ya hana kusantar wurin ibada yayin da aka sha ta.[7] Daga ƙarshe ne kuma ya sauƙar da hani kai tsaye game da shan giya inda aka ce:

“Ya ku waɗanda suka yi imani, ku sani cewa, giya da caca da gumaka da ƙyaurayen duba ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nisance su don ku rabauta (Alƙur’ani; 5:90).

A wannan ayar an bayyana wa masu imani munanan ayyuka da ake buƙatar mumini ya nisance su. Kuma duk al’ummar da ta rungume su za ta faɗa cikin masifa da rashin kwanciyar hankali. Ayar ce kuma ta zo da haramcin shan giya kai tsaye.

Akwai hadisai da dama da suka tabbatar da haramcin shan giya da kuma abin da ake kira da giya. Annabi S.A.W. yana cewa: “Duk abin da ke bugarwa giya ce, kuma kowace irin giya haramun ce” (Muslim ne ya ruwaito shi).

A wani hadisin kuwa cewa ya yi:

Allah ya tsine wa giya, masu shan ta, da waɗanda suka zuba ta, da waɗanda suka sai da ita, da waɗanda suka saye ta, da waɗanda suka tatso ta, da waɗanda suka ɗauki kayan da ake tatsarta, da waɗanda suke ɗauke ta, da waɗanda aka kai wa ita, da waɗanda suka samu kuɗi a gare ta” (Abu Dawuda, da Al-Hakem a isnadi ingantacce, suka kawo shi)

Yayin da aka dubi waɗannan nassoshi, za a tarar cewa, ƙin bin su sau-da-ƙafa keta shara’ar Musulunci ne, wato fanɗarewa faɗar Allah da annabinsa ne. Duk da haka, an ci karo da waƙoƙin da suka yi kira da a sha gida. Alhaji Mamman Shata Katsina ya waƙe giya. Har ma cewa ya yi:

Jagora: Ka ji karatun masu bugun ruwa,

Waɗanda...

‘Y/Amshi: Ke zikiri a Kuloniya.

            A sha ruwa ba laihi ba ne.

 

Jagora:  A nan muke sallarmu ta Juma'a,

Mu tattara kayanmu mu kai Neja,

Ku sha ruwan nan...

‘Y/Amshi: Ba laihi ba ne.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

 

Jagora: Ruwa na kwalba ba laihi ba ne,

Ai kun ga...

‘Y/Amshi: Alhaji Shata sha yake.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

 

Jagora: Yara mu koma wasa Kuloniya,

Mu tashi kana mu koma Neja,

‘Y/Amshi: Nan ne muke zikirinmu na Juma'a.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

 

Jagora: Malam ka sha ai ba laihi ba ne,

Ga taka ga tau...

‘Y/Amshi: Kowa ya aje.

A sha ruwa ba laihi ba ne.

Idan muka nazarci waɗannan ɗiyan waƙar za a ga yadda mawaƙin ya yi fito-na-fito da dokokin Allah da Manzonsa. Allah ya haramta, shi kuma ya halatta. Dubi yadda mawaƙin ya ce a sha giya ba laifi ba ne, bayan Annabi S.A.W. ya ce kada a sha, a inda yake cewa: “Kada ku haɗa fulawa da dabino gaba ɗaya, kuma kada ku haɗa busasshen tafarnuwa da dabino sam-sam, ku bar su idan an niƙa su.”

Yayin da aka niƙa su, nan take suna bugar da wanda ya sha su. Don haka ne Annabi ya umarci masu imani da kada su sha a haɗe yayin da suke niƙe, kamar yadda Munhajul Muslimu Jadawali na uku: Abinci da Abinsha ya nuna.

Hasali ma mawaƙin ya bayyana cewa shi ma yana shan giyar tare da yaransa. Akwai hadisai da dama da suka nuna haɗarin Musulmi ya mutu yana shan giya, ko da bai halatta ta ba. To ina ga wanda ya halatta shan ta? Daga cikin ire-iren waɗannan hadisai akwai wanda Ibni Abbas ya ce: Manzon Allah S.A.W. ya ce:

Duk wanda ya mutu yana cikin ɗabi’ar shan giya bai tuba ba, zai tarar da Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki tamkar wanda ya bauta wa gumaka (Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin).

A wata waƙar ta mawaƙin da ake kira Horo/Horu, an ga baitukan da suka nuna ba laifi ba ne shan giya da ma cin mushe. Mawaƙin na cewa:

Jagora: Arnaaa ku sha giya ku ci mushe,

Aljanna mai rabo zai sama.

A wani wuri kuwa, har ya nuna ma kashi ne ga mutum ya sha giya ‘yar kaɗan kuma ta wahalshe shi. Yana cewa:

Jagora: Kowa ya sha giya yai yi amai,

Ba ɗan halas ba ne, shege ne!

 

Jagora: Su wane ‘yan giyan ƙarya ne,

Shegu, kwalba guda take ka da su.

3.4 Goyon Bayan Sata

Abubakar (2015, p. 431) ya bayyana cewa, sata “tana nufin ɗaukar abin wani ba da saninsa ko izinin ba.” Sata na nufin ɗaukar wani abu da hukuncin shari’a ko hankalin tuwo bai mallaka wa wanda ya ɗauka ba, tare da amfani da shi ko musanyensa da wani abu mai daraja kwatankwacin na kuɗi ko kuma mai amfanarwa, ba tare da izinin wanda ko waɗanda ke da mallakin abun ba.

Sata ta kasu zuwa nau’uka daban-daban. Sun fi danganta da salon yadda aka gudanar da satan. Fitattu daga cikinsu sun haɗa da:

i.        Cuta[8]

ii.      Damfara[9]

iii.   Fashi[10]

iv.   Fizge/Wabce/Fauce[11]

v.      Ƙwace[12]

vi.   Sane[13]

Sata babbar abar ƙyama ce a farfajiyar Hausa da Hausawa, tun ma kafin bayyanar addinin Musulunci. Sauyawan al’amurra da cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu sun wanzar da taɓarɓarewar tarbiyya da ƙoƙarin neman tara abin duniya ido rufe. Ta kai ga fanɗararru marasa kishin kansu cikin al’umma sun tsunduma a fagen wannan ta’addanci.

Yayin da addinin Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa, sai ya ƙara ƙarfafa wa Hausawa ƙyamar wannan muguwar sana’a. Musulunci ya zo da dokoki domin kawar da duk nau’o’in sata. Allah na cewa:

Ɓarawo kuma da ɓarauniya sai ku yanke hannayensu ya zama sakamako ne na abin da suka aikata, (wannan horo ne) daga Allah. Allah kuwa mabuwayi ne Gwani. (Alƙur’ani, 5:38).

A addinin Musulunci ta kowace fuska ana ƙoƙarin kare dukkanin al’umma ta yadda za a zauna cikin aminci game da dukiyoyi da rayukan al’umma. Ita kuwa sata, mugun hali ce da ke haifar da rashin kwanciyar hankali da salwantar rayuwa a tsakanin al’umma. Don haka ne shari’a ta tanadar da hukuncin yanke hannun ɓarawo wanda zai hana watsuwar irin wannan muguwar ta’asa a tsakanin al’umma.[14] Allah na cewa: “Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar cuta” (Alƙur’ani, 2: 188).

Ayar tana tabbatar wa masu imani cewa, cuta haram ce. Ba ya halatta ga Musulmi ya yi zalunci ta hanyar zaƙin baki ko dabara. Haka kuma, bai halatta ya yi jagora don a cuci wani ba.

Duk da irin waɗannan dokokin da Allah Maɗaukakin Sarki ya shimfiɗa domin samar da kyakkyawan zamantakewa da aminci a doron ƙasa, an samu gungun mawaƙa da ke jayayya da dokokin cikin lafuzzan waƙoƙinsu. Bunza, (2014) ya kawo baituka da dama daga bakin Alhaji Muhammadu Gambo Fagada. Gambo ya bayyana ƙarara cewa:

Jagora: Don waɗanda ka sata nay yi ganga

            Ba do wani sarki mai naɗi ba.

(Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Tsoho Tudu)

A cikin waƙarsa ta Nazaƙi kuwa, an ga yadda hirarsu ta gudana da Nazaƙi bayan ya tuba daga sata. Sannu a hankali har Gambo ya sake zuga shi yadda har sai da ya dawo satan. Gambon da kansa ya bayyana cewa:

Ɓarawo in ina kusa ba tuba yakai ba,

Ko ya aje gemu, ko ya yi saje,

Ko ya fidda farin gashi ga kaina,

In Gambo na kusa ba tuba yakai ba,

Ba ko batun shegantaka ba.

(Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Nazaƙi)

A wannan ɗiyan waƙa, sai da ya jaddada cewa, batunsa ba “batun shegantaka” ba ce kawai. Wato dai haƙiƙanin gaskiya yake faɗa cewa idan yana kusa ɓarawo ba ya tuba domin kuwa zai ziga shi ya hana shi tuban.

Wasu makaɗan sukan yi waƙoƙin yabo ne ga ɓarayin. Misali Alhaji Mamman Shata ya yi wa wani ɓarawo mai suna Mamman Ɗan’yarbayye waƙa, a inda yake cewa:

Jagora: Mai hannun taɓa ƙofa in an bacci,

Masu samame baƙon Ɗanmani.

Na faɗa maka Mamman.

In dai ka ɗauko sa’a,

Har ka buɗe ƙofa,

Ka tarar an bacci,

To zari akwati tsakiyar shi ya fi kaya.

Na saman hoto ne,

Na ƙasan maganin ƙwari ne.

Tafi zari akwatin tsakiyar shi ya fi kaya.

Na Abdu ƙyale dangi sai an bacci,

Iyalin Mamman, waɗanda ba su so a yi haske,

Su sun fi so a tabka duhu da ruwa yaf-yaf-yaf.

Wani don ya taka kara bai mai ƙara ba,

Sannan ganyen ganji duk ya bi ƙasa.

(Alhaji Dakta Mamman Shata: Mamman Ɗan’yarbayye)

A waɗannan ɗiyan waƙar, mawaƙin ya yabi ɓarawon tare da ba shi shawarar yadda zi gudanar da sana’arsa ta sata. Wannan ya haɗa da yi masa ishara ga irin lokuta da yanayi da dabarun da zai bi wajen yin satar, da kuma nau’in abin da zai sata da ya fi saura daraja. Hakan kuwa karan-tsaye ne ga dokokin addini. Hadisin Manzo (S.A.W.) ya bayyana cewa:  Ɓarawo ba ya sata a lokacin da yake da imani” (Buhari ne ya ruwaito hadisin).

Allah Maɗaukakin Sarki ya kawo nau’in hukuncin da ya dace a zartar wa masu fashi da makami, a inda yake cewa:

Ba wani abu ne sakamakon waɗanda suka yi wa (Musulmi masu bin) Allah da manzonsa fashi ba, kuma suke tafiya a bayan ƙasa da ɓarna ba, sai kawai a kashe su ko kuma a tsire su ko a yanke hannayensu da ƙafafuwansu a tarnaƙe, ko kuma a kore su daga ƙasa. (Yin) wancan ƙasƙanci ne a gare su a duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma. (Alƙur’ani, 5:33).

Allah ya bayyana mana cewa masu yin fashi da makami suna ƙoƙarin ɓata tsarin Allah da Manzonsa ne, saboda aiwatar da fashi ya kauce wa hanyar gaskiya da adalci, waɗanda Musulunci ke ƙoƙarin tabbatar da su a doron ƙasa.

3.5 Goyon Bayan Kisan Kai

Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa:

Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwamini a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya tanadi azaba mai girma a gare shi (Alƙur'ani, 4:93).

An jiyo Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago[15] yana cewa:

Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,

Ba kukan tuwo ba,

Ba na hura ba...

‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi,

Suna kirarin banza.

 

Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin

‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake....

A wani wuri yana cewa:

Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma.

            Ɗan Abdu...

‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.

(Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi laakari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:

i.        Kusheyi

ii.      Lahira a kai miki gawa

iii.   Lahira tana yin baƙo

iv.   Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu[16]

Gambo ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:

Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,

            Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,

            In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,

            Don wagga ba sata ta ba Gambo.

(Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

3.4 Hani ga Bautar Ubangiji

Ko bayan kira zuwa ga aikata ɓarna da fasadi, akwai misalan ɗiyan waƙoƙi kuma da ke kira ga barin bautar Ubangiji. Na biyu a cikin shika-shikan Musulunci ita ce salla. Tana da matuƙar muhimmancin da har ya kasance kadarko tsakanin mutum da kuma shirka da kafirci. Duk da haka, sai ga ɗiyan waƙa da ke hani ga yin salla:

Bayarwa: Ɗan Abdu ban da sallas swahe,

‘Y/Amshi: Domin yawan sallan nan yana rage maka ƙarhi.

(Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

4.1 Sakamakon Bincike

Ta la’akari da nassoshin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. da kuma ƙumshiyar wasu waƙoƙin baka na makaɗan Hausa, za a a iya cewa, mawaƙa na wuce gona da iri a waɗansu lokuta. Yawanci hakann na faruwa ne yayin da suka yi ƙoƙarin adanta waƙoƙin nasu domin burge wanda aka yi wa waƙar da kuma sauran masu sauraro. A haka ake samu ɗiyan waƙoƙin sun yi wa dokokin Musulunci karan-tsaye.

A wannan nazarin an fahimci cewa duk wani aikin da ɗan’adam ya aikata wanda Allah da manzonsa suka yi hani da shi, yin haka nau’i ne na fanɗare wa dokokin Allah. Ya zama tilas kowane Musulmi ya nemi ilimin duk wani lamarin da ya shafi rayuwarsa, (kamar yadda mai Ahalari ya bayyana) don gudun auka wa fushin Ubangiji. An kuma fahimci cewa, a Musulunci kowane irin al’amari an ɗora shi a kan mataki-mataki. Wannan ne ya wajabta wa kowane Musulmi ya yi umurni da aikata alheri da kuma hani ga mummunan aiki gwargwadon ƙarfin ikon mutun.

4.2 Kammalawa

Yin fice da waƙoƙi suka yi wurin ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa, ba shi ke nuna ba a samun fanɗarewa a cikinsu ba. Nau’ukan fanɗarewa da ake samu cikin waƙoƙin Hausa sun shafi ziga zuwa aikata abin da Ubangiji ya hana, ko izgilanci ga abubuwan da Musulunci ya zo da su, ko kuma hani ga abin da Ubangiji ya yi umarni da a aikata. Abu ne mai kyau manazarta su riƙa zaƙulo ire-iren fanɗarewa da ake samu a cikin waƙoƙi domin faɗakar da al’umma da su kansu mawaƙan. Malamai da ke jagorantar nazarce-nazarcen waƙoƙi a makarantu kuwa, ya kamata su mayar da hankali wajen yin shiri na musamman na faɗakar da ɗalibai ta fuskokin da suka dace yayin da aka ci karo da ire-iren baitukan fanɗarewa a cikin waƙoƙin da suke nazarta. Gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa ma na da rawar takawa wajen samar da ƙa’idoji da tsare-tsaren tace waƙoƙi kafin sakinsu. Haɗakar waɗannan za su tabbatar da al’umma ba ta rinjayu da kiraye-kirayen waƙoƙin fanɗara ba zuwa taɓewa.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan waƙar baka ta Hausa. Gaskiya Corporation Limited.

Abubakar, A. (2015) Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company LTD.

Al-Munajjid, M.S. (2004). Muharramat: Forbidden matters same people take lightly. International Islamic Publishing House, Saudi Arebia.

Bunza, A.M. (2014). In ba ka san gari ba saurari daka: Muryar nazari cikin tafashen Gambo Elkods Printing Hausa.

Chiromawa, U.A.U. (n.d.). Dalilin kiɗa a cikin Alƙur'ani da hadisi.

Gusau, S.M. (1984). Nazarin zaɓaɓɓun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, littafe na ɗaya.

Ibrahim, M.S. (1983). Kowa ya sha kiɗa. Longman Nigeria Limited.

Magaji, A. (2016) Kassu Zurmi da waƙoƙinsa. Spectrum Books Limited.

Muhammad, Y.M. (2005). Adabin Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited

Sani A-U. & Jaja, M.B. (2019). Zamani Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannu Addini da Zamani. In The Nasarawa Journal of Humanities. Vol.7, Number 1&2,  Pp. 257-268. ISSN: 1118-6887.

Shehu, M. & Sani, A-U. (2019). Intra-Religious Conflicts within the Hausa Hausa-folk. In EAS Journal of Humanities and Cultural Studies, Volume-1, Issue-3. Pp 145-150. ISSN: 2663-0958 (Print) & ISSN: 2663-6743 (Online) Available at: https://www.easpublisher.com/get-articles/344.  

Umar, M.B. (1987). Dangantakar adabin baka da al’adun gargajiya. Kamfanin “Triumph” Gidan Sa’adu Zungur.[1] Rubuce-rubuce da dama sun kawo bayanai game da zuwan Musulunci ƙasar Hausa. Ana iya duba Shehu and Sani, (2019) ko Sani da Jaja, (2019) domin samun ƙarin bayani.

[2] Akwai maganganun malaman Musulunci mai tarin yawa game da wannan batu.

[3] Yayin da aka nazarci wannan ayar za a tarar cewa Allah ya haramta zina da duk wani abu da zai haddas Musulmi ya kusanci aikata zinar, kamar dubin wadda ta kasance aurenta ya halatta a tsakaninsu da ita, da jin daɗin zancenta.

[4] Mazinata da suku mutu ba tare da sun tuba ba kuwa, za su furkanci azaba mai raɗaɗi kamar yadda addini ya nuna.

[5] Dalilin da ya ƙara danganta kunya da imani shi ne, dukansu suna kira zuwa ga alheri da kuma nisanta alumma daga miyagun ayyuka. Imani yakan kai Musulmi da su yi biyayya ga dokokin Allah, tare da nisantar zunubai, kamar yadda ya zo a cikin Munhajil-Muslimu (kashi na 7, Kunya a cikin Mutane).

[6] Suna tambayar ka daga giya da caca. Ka ce: A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfanoni kaɗan ga mutane. Kuma zunuban su ne mafi girma sama da amfaninsu” (Alƙurani; Suratul Baƙara, 2:219).

[7] “Ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kusanci sallah alhali kuwa kuna masu maye, har sai kun san abin da kuke faɗa” (Alƙurani, 4:43). Alƙur’ani ya kuma yi nuni da munin shan giya inda yake cewa: “Abin sani, Shaiɗan yana son kawai ya jefa gaba da ƙiyayya a tsakaninku, cikin hanyar giya da caca, ya kuma hana ku zikirinn (ambaton) Allah, kuma da salla. Yanzu ba za ku bari ba! (Alƙurani; 5:91).

[8] Cuta na nufin duk wani nau’in tauye mudu ko danne haƙƙi ko cin amana da zai kai ga mutum ya mallaki wani abu ko ya yi amfani da wani abin da a shari’ar addinin musulunci ko ƙa’idar zamantakewa da hankalin tuwo, bai kamata a ce ya mallaki abin ba.

[9] Damfara na nufin amfani da dabaru da hikimomi domin raba wani ko waɗansu da wani abin da suka mallaka yayin da suka faɗa tarkon siddabaru ko wala-walar da aka shirya musu. Masu zalama sun fi faɗawa tarkon ‘yan damfara.

[10] Fashi amfani ne da makami domin ƙwace wa wani mutum ko waɗansu mutane abin da suka mallaka.

[11] Fizge salon sata ce da wanda ke yin ta ke wafcewa ko fizge abin da ke hannun wani sannan ya sheƙa da gudu ko ya yi waɗansu dabarbarun ɓacewa daga idon masu abu da ‘yan kwalala.

[12] Ƙwace na nufin amfani da ƙarfin tuwo domin karɓe abin da wani ko waɗansu suka mallaka ba tare da son zuciyarsu ba. Wanda aka fi ƙarfi ko ƙarfin zuciya ake yi wa ƙwace.

[13] Sane na nufin amfani da hikima da ƙwarewa wajen sace abin da ke jikin mutum ko wanda ke riƙe a hannunsa ko cikin jakarsa ko masaki ko maɗauki da ke tare da shi ba tare da saninsa ba, wanda a sababbiyar al’ada ya kai a ce ya farga a lokacin da za a ɗauke abin.

[14] Aiwatar da hukuncin zai zama tsawatarwa ga wani da ke sha’awar ta, ta la’akari da abin da ya auku ga wanda aka zartar masa da hukuncin. Ta haka sai ya kasance babu ɓarawo a tsakanin al’umma, domin tsoron datse hannu da kuma dawwamammiyar kunya a tsakanin al’umma. Hakan zai sa a samu aminci da rashin fargaba a duk faɗin ƙasa.

[15] Asalin sunan Shago shi ne Alhaji Abubakar Yarkofoji. An fi sanin sa da Shagon Bakura/Shagon Mafara.

[16] Wannan ita ce fahimtar [Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, Keɓantacciyar tattaunawa, 15 ga watan Oktoba, 2023].

Post a Comment

0 Comments