Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Addu'ar Da Ake Yi A Bayan Sallar Farilla Ita Ake Yi A Bayan Sallar Nafila?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu. Malam na san kusan dukkan addu'o'in da ake yi bayan an yi sallama a sallar farillah. Shin wasu addu'o'i ake yi bayan an gama na nafila. Shin iri ɗaya ne ko da bambanci? In da bambancin mene ne, kuma wasu addu'o'i ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu wa Rahmatullah, ɗan uwa ya tabbata daga Sahabin Manzon Allah Thaubaan Allah ya qara masa yarda ya ce: Idan Manzon Allah ya idar da sallarsa ya kasance yana yin istigfari sau uku, sannan sai ya ce:

"اللَّهُمَّ أَنْتَ السَّلامُ، ومِنْكَ السَّلامُ، تَباركْتَ يا ذَا الجلالِ والإِكْرامِ".

Alwaleed daga cikin maruwaita hadisin ya tambayi Al'auza'iy cewa: "Ya ya istigfarin yake? Sai Al'auza'iy ya ce za ka ce ne: Astagfirullah, Astagfirullah". Muslim ne ya ruwaito a hadisi mai lamba ta (591).

Wannan istigfari sau uku, da kuma wannan zikiri ta "ALLAHUMMA ANTAS SALAM", ya haɗa sallar farilla da ta nafila, domin maruwaita hadisin ba su faɗi cewa a farilla kaɗai ko a nafila kaɗai Manzon Allah yake yin wannan zikiri ba, wato duk sallar da mutum ya idar ta farilla ko ta nafila yana da damar karanta su, saboda hadisin ya nuna cewa Annabi yana yi ne da zarar ya idar da sallah, ba tare da keɓance sallar nafila ko ta farillah ba.

Amma sauran azkar ɗin da ke biyo bayan waɗanda suka gabata ɗin nan, wasu malamai sun nuna cewa sun keɓanta ne ga sallolin farilla, saboda hadisan da suka zo da su hakan suke nunawa.

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments