Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsayin Yin Wuturi Da Raka'o'i Uku Sallama Ɗaya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, ya hukuncin yin sallama ɗaya a cikin sallar shafa'i da wutiri? Ma'ana ka haɗa su guda uku kayi tahiya ɗaya da sallama ɗaya, ya halasta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salám, ya halasta a yi sallar wuturi da raka'o'i uku, ko da raka'o'i biyar, ko da raka'o'i bakwai, ko da raka'o'i tara.

Amma idan mutum zai yi wuturi da raka'o'i uku ne, to tana da siffofi guda biyu ne kamar haka:

1. Siffa ta farko ita ce mutum ya jero duka raka'o'i ukun da yin tahiya guda ɗaya a ƙarshe, sai ya yi sallama.

2. Siffa ta biyu kuma ita ce ya yi tahiya ya yi sallama a raka'a biyu, sannan ya miƙe ya yi wuturi da raka'a ɗaya.

Dukkan waɗannan siffofi Sunnah ta zo da su, idan yau mutum ya yi wannan siffar gobe kuma ya canja, to hakan ya yi kyau.

Ya halasta mutum ya yi ta da sallama ɗaya da tahiya ɗaya, amma ba da tahiya biyu ba, saboda idan ya yi ta da tahiya biyu, to ta yi kama da sallar Magriba, kuma haƙiƙa Manzon Allah ya hana a kamanta ta da sallar Magriba.

Dubi Assharhul Mumti'u Ala Zhádil Mustaƙni'i (4/ 14 - 16) don ƙarin bayani.

Allah S.W.T ne mafi sanai.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments