Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin wajibi ne miji ya fitarwa matarsa wacce ya saka saki mai kome zakkar fidda kai?

 T𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin wajibi ne miji ya fitarwa matarsa wacce ya saka saki mai kome zakkar fidda kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Zakkar fidda kai tana wajaba a kan mutum, da waɗanda wajibi ne akansa yaciyar dasu, kamar matarsa da 'ya'yansa, saboda hadisin da Abu dauda da baihaƙi da darul ƙudni suka ruwaito daka Abdullahi dan Umar yardar Allah takara tabbata agaresu daka Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Ku bayar da zakkar fidda kai ga kawunanku da waɗanda kuke ciyarwa) sai dai wannan hadisi za'ifine baihaƙi da Annawawi da ibnu hajar da wasunsu sun raunanashi.

Almaj mu'u (6/113) da Talkisul habeer (2/771).

Malaman lajnatul da'imah (9/367) sukace: Zakkar fidda kai tawajaba a kan mutum da kuma wanda cidasu yake wajibi akansa, daka cikinsu akwai matarsa, saboda wajabcin ciyar da ita dake kansa.

Mace idan mijinta yasaketa saki mai kome, tana cikin hukuncin matar aure dole miji yabata gurin zama da kuma tufatar da ita, matukar tana cikin iddah, zakkar fidda-kai kuma tana bin wajabcin ciyarwane, matukar wajibi ne ciyar da matar da'aka saketa saki mai kome to haka yimata zakkar fidda-kai wajibi ne.

Annawawi a cikin Almaj mu'u (6/74) ya ce: Wajibi ne yiwa matar da'aka saka zakkar fidda kai, kamar yanda ci da'ita yake wajibi.

Wasu malaman suntafi a kan cewa bawajibi bane miji ya fitarwa da matarsa zakkar fidda kai, itama wajibace a kanta, wannan ita ce mazhabar Imamu Abu hanifa rahimahullah shaik usaimin yazabi wannan ra'ayin.

Abun da ya fi kuma ya kamata shi ne miji ya dauki abun da yafi, ya fitarwa da matarsa daya saka saki maikome zakkar fidda kai, musamman kasancewar zakkar fidda-kai wata abace sassauka, amafi yawancin lokuta ba ta yiwa miji wahalar fitarwa.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments