Wasiyyar Mutan Makka

    Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

    Nakan tuna da da safe,

    Wanka ma ban iya ba,

    Mutan Makka ke ki ke min.


    Komai sanyi da zafi,

    Ba kya gajiya gazawa,

    Ki shafan mai da kanki.


    A baki ki ban abinci,

    Riga mai kyau ki sa min

    Ki ce da Amina yata.


    "Riƙe hanayensa sosai,

    Titi ku kula da mota,

    A Mubi ku gaida Laure.


    Ko ya ce za shi kwana,

    Ƙafarki ƙafarsa kin ji,

    Hajiya ta hana ku dawo.


    Kafin La'asar na gan ku,

    Makaranta don ku zauna,

    A ta allo kun yi hadda".


    Kakata Hauwa giwa,

    Akwai fara'a cikinta,

    Mai kyauta ta fi kogi.


    Ina ƙaunar ganinta,

    Gidanta in je na kwana,

    Nai wasa in ta murna.


    In na waiga a baya,

    Nakan tuna ga ni ga ki,

    Kina yi min karatu.


    Ki kan ce rayuwan nan,

    Shi mai hikima a kullum,

    Ke ginin goben tun yau.


    Ban mantawa ki kan ce,

    "Riba ƙarama ta yanzu,

    Kar ka yadda ta hila ce ka.


    Riba nasara ta gobe,

    Kar ka kau da idonka kanta,

    Zama mai haƙurin jiranta..


    Mai halayya ta randa,

    Mutum ne mai dabara,

    Bai ɓarnar dukiyarsa.


    Damina ko ta yi nisa,

    Shi indadaro halinsa,

    A ba shi yana zubarwa,


    Ɓarnar da ya saba yi ce,

    Ke sa shi wuni a bushe,

    Daure ka kula ka lura."


    Mutan Makka jami'a ce,

    Na ɗau darusa wajenta

    Kuma na amfana sosai.


    Takan ce duniya yau,

    "Sai kai haƙuri da kowa,

    Bare dangi jininka".


    Takan ce babu shakka,

    "Aiki na nan a gona,

    Mai gona sai ya shirya".


    Sai yanzu na gane zancen,

    Yau zumunci ya fi tsumma,

    Wuyar ɗinki da gyara,


    Ka kamo nan ya dare,

    Ka ɗinke can ya ɓarke,

    Sai an jure zumunci.


    Nakan tuna ko da yaushe,

    Ki kan ce, "shi zumunci,

    Ba riga ne ba shi sam,


    Da zaka saka ka sauya,

    Ko ko hula ta kanka,

    Ko takalmin ƙafarka.


    In ana maganar zumunta, 

    Ba a maganar abota,

    Ko ma maganar ƙawance.


    Abokai ko ƙawaye,

    Mutum ke zaɓi nasa,

    Dangi Allah ya baka.


    Su yi ma kar su yi ma,

    Zumunci yi ma kowa,

    Kowa haƙƙinsa ba shi.


    Kar ka ce sai mai sukuni,

    A dangi zaka yi wa,

    Don ya rama ma a gobe..


    Juriya Allah ya baka,

    Kai ne babban cikinsu,

    Haƙuri tilas ka koya.


    Wasiya ce nake ma,

    Haƙuri dage ka ƙara,

    Allah zai baka lada.


    Na sanka kana da ƙwazo,

    Ko da an sosa ranka,

    Daddage kar ka rama.


    Juji ne shi fa babba,

    Haƙuri na ƙasa ya gada,

    Ƙasa na shanye komai.


    Su mai da ruwan kwata duk,

    Ƙasa na sha cikinta,

    Allahu Ya taimake ka.


    Alƙali ne da sannu,

    Haƙuri matuƙar ka yi shi,

    Zaƙi na zuma gare shi.'


    Mutan Makka mai zumunci,

    Azumi uku ga shi ba ki,

    Har gobe ina ta kuka.


    Allah don Annabina,

    Uwata Hajiyata,

    Aljanna ka ba ta gobe.


    Fir'dausi gidan aminci,

    Ka sake haɗa mu Allah,

    Mu rayu cikin salama.


    Allah don Mai Madina,

    Amsa mini addu'ata,

    RahamarKa Ka ba mu tare.

    Malam Khalid Imam
    08027796140
    khalidimam2002@gmail.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.