Ticker

6/recent/ticker-posts

Kabari

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

 Wasu don shagala da mulki,

Maƙabarta sun ka yanka.


Su sassaidar da filin,

Su sami kuɗi na harka.


Maƙabarta dai gida ne,

Ga kowa babu shakka.


Komai girman gidanka,

Ƙarshe can za a kai ka.


Gida ne babu taga,

Kabari haka za a saka.


Ɗaki ne babu falo,

Dangi ne masu son ka.


Za sui himma su kai ka,

Duk da son da su ke gare ka.


Ba mai canjinka ranar,

A dukkan 'yan uwanka.


Matarka da ke gidanka,

Ita ma ɗin ba ta bin ka.


'Ya'yanka da ma barori,

Da su duka za a kai ka.


Abokai masu maula,

Masu ma layi gidanka.


Masu ƙaryar naka ne su,

Ba mai saurin tunaka.


Za a tona ƙasa idonsu,

Suna kukan rashinka.


Rami ne bai da girma,

Za a tona iya tsayinka.


A ranar sai halinka,

Bai mai kula matsayinka.


Ka yi sarki ka yi gwamna,

Kai ta shafa sai halinka.


Shi ne zai ma amana,

Ya ce shi zai raka ka.


In kowa ya ƙi bin ka,

Shi tilas ne ya bi ka.


Ba sanayya babu kara,

Shi zai shaida a gunka.


A can ba mai taya ka,

Noma girbi da shuka.


Khairan sharri ruwanka,

Adashi ka kwashe naka.


Ba alƙali da Malam,

Kabari ƙarshen gidanka.


Kafin in tsinki kaina,

Cikin kabari na farka


Kuskurena Rabbu shafan,

Kafin in zo gare Ka.


Don Ɗaha mijin Khadija,

Tushensa yana a Makka.


A halittu ba kamarsa,

Domin shi ne fa naka.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments