Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwanakinmu

 1. Kwanaki na mana gwalo,

       Wasu na shagali da murna.


2. Ga ƙasa na ambatonmu,

     Mun shagalta da cin amana.


3. Ga shi ba ta ma sanarwa,

             Mutuwa, balle mu auna.


4. Kuma ba ta ƙara loto,

              In ta zo balle mu zauna.


5. Kwanaki na yaudararmu,

       Ga shi babu zaman lumana.


6. Duniyar nan babu tabbas,

             Ko da me ja kan batuna?


7. Sai ka wayi gari cikinmu,

            Yamma ba kai in ka auna.


8. Wasu sai ko a tashi ba su,

           Haihuwarsu ta zo da ƙuna.


9. Daga nan sun ɗauki layi,

           Kwanakinsu a nan ya zana.


10. Tun ana ɗan baka mama,

            Har ka girma ka je Madina.


11. Sai batun aure ya taso,

                  Sai ka auri ɗiyar Amina.


12. Shekara kafin ta dawo,

                Haihuwa ce har da suna.


13. Daga nan ka zama Baba,

                   Sai iyalai duk su baina.


14. Sai ko tsufa ta rufe ka,

            Daga nan mutuwa ka auna.


15. Kwanaki sun baka dama,

                 Sai abin da kayo a duna.


16. Ihiwani ƙwarai mu farka,

                   Kwanaki tafiya da rana.


17. Allah ba mu sa'a gaba ɗai,

   Duk mu ɗunguma can a aljanna.

Ta

Mohammed Bala Garba

23 July, 2022.

Sabuntawa

29 March, 2023.

Post a Comment

0 Comments