Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanda yake azumin kaffarar kisan kai shin idan ya samu kansa ahalin tafiya zai ajiye azumi ko yaya.?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Wanda yake azumin kaffarar kisan kai shin idan ya samu kansa ahalin tafiya zai ajiye azumi ko yaya.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Kaffarar kisan kai na kuskure shi ne 'yanta baiwa mumina, idan mutum bai samu baiwaba ko kuɗin sayenta, sai ya yi azumin wata biyu ajere, Bai halatta mutum yatsallake 'yanta baiwaba yakama azumi sai idan bai samu baiwarba ko kuma bashi da kuɗin sayenta.

Ya zo a cikin Mausu'ah fiƙhiyyah (10/129) Azumi yana zuwane amataki na biyu idan mutum baida halin 'yanta baiwa ko kuɗin sayenta, kamar yanda ya zo a cikin fadin Allah madaukakin sarki.

(ومن قتل مؤمنا  خطأ فتحرير رقبة مؤمنة)

Duk wanda yakashe rai abisa kuskure zai 'yanta baiwa mumina.

Harzuwa fadin Allah madaukakin sarki.

(فمن لم يجد فصيام شهرين متتابعين توبة من الله وكان الله عليما حكيما)

Duk wanda bai samu halin 'yanta baiwaba zaiyi azumin wata biyu ajere tubane zuwa ga Allah, Allah ya kasance masanine a kan komai kuma mai hikima cikin dukkan al'amura).

 

Wanda yafara azumtar wasu kwanaki na kaffarar kisan kai, sannan sai wani uzuri nashari'a yafado masa, kamar rashin lafiya ko tafiya, ko haila ta zo mata idan macece kota haihu, zai cika a kan abunda ya azumta abaya dazarar uzurin yakau, bazai sake sabon lissafiba zai dorane a kan lissafin baya kafin uzurin yariskeshi.

Shaik Usaimin rahimahulla ya ce: Idan mai azumin kaffara yasha azumi saboda wani uzuri daya halatta masa yasha azumin, kamar rashin lafiya ko tafiya, to jerantawarsa bata yanke ba, kaffarar ziharice, ko kaffarar saduwa da macene darana a cikin Ramadan, ko kaffarar kisan kai, idan ya yi tafiya yasha azumin to jerantawar azuminsa bai rushe ba, domin tafiya ta halatta masa shan azumi, amma dazai kirkiri tafiyar dan ya yi wayan shan azumin, to anan sai a ce haramunne yasha azumin wajibi ne yayishi, domin ayyukan wajibai basa faduwa daka kan mutum tahanyar wayau, Idan kuma yaki kame bakinsa to wajibi ne yasake sabon lissafin azuminsa.

Ya zo afatawa lajnatul da'imah (21/320). Asali wajan sifar azumin kaffarar kisan kai shi ne jeranta azumin, ba abunda zai yanke wannan jerantawar sai dai idan na lalurane, kamar rashin lafiyar dabazai iya azumi ba, kamar mai haila ga mace, wannan baya yanke jeranta azumin kawai mutum zaici gaba a kan wanda yariga yayisu.

WALLAHU A'ALAM.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments