Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Amfani Da Maganin Inhela Ga Mai Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin amfani da maganin fesa iska a cikin bakin mai azumi da rana (wato, inhela), saboda ciwon ƙuncin ƙirji ko wahalar numfashi (Asma)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Hukuncinsa shi ne halacci; idan har lalura ta buƙatar da mutum zuwa ga hakan, saboda fadin Allah Mabuwayi da daukaka a cikin "suratul An'aam ayata 119":

وَقَدْ فَصَّلَ لَكُم مَّا حَرَّمَ عَلَيْكُمْ إِلَّا مَا اضْطُرِرْتُمْ إِلَيْه

Ma'ana: "Kuma ya muku bayani na dalla-dallan abin da ya haramta a kanku, sai dai wanda lalura ta buƙatar da ku zuwa gare shi"

Kuma saboda kasancewar inhela baya kamantacceniya da ci ko sha, sai ya yi kama da jinin mutum da ake dauka don aunawa ko bincike, ko kamar allurar da ba a sanya abinci a cikinta ba.

Duba cikin littafin: TUHFATUL IKHWAN BI AJWIBATIN MUHIMMATI TATA'ALLAƘU BI ARKAANIL ISLAAM.

MAJMU'U FATAWA WA MAƘAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 265).

Allah ta'ala ya sa mudace.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments