Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallar Tahajjud Ga Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam shin mata za su iya zuwa masallaci sallar Tahajjud?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Hadisai masu yawa sun zo kan zuwan mata masallaci don sallar Tahajjud ko Tarawihi. Sayyidina Umar Allah ya ƙara masa yarda ya sanya limamai guda biyu : Ubayyi ibn Ka’ab da Tamimud Dari daya na maza limanci ɗaya nama mata. Kuma duk sallar da ake yi mata na halarta, kuma raka’a goma sha ɗaya suke yi (Muwatta) Hakanan ma Tuhajjudi da ake zuwa cikin dare suma mata ya halasta suje amma da izinin mazajensu ko iyayensu in ba su da aure iyayensu za su tambaya kafin su fita zuwa masallaci, amma in ana tsoron fadawa cikin fitina to babanta ya kaita ko mijinta ya kaita ko kuma ta yi agida in za ta iya yi, baba ko miji kar yahana ‘‘yarsa ko matarsa zuwa masallaci sallar Tahajjudi koTarawihi tun da ya zo a cikin Bukhari wanda manzon Allah (s.a.w) ya ce ‘‘Kar ku hana mata bayin Allah zuwa masallaci in matar daya daga cikinku ta nemi izinin zuwa masallaci to kar yahanata. (Bkhari).

Amma kuma duk da haka da za ta yi agidanta ya fi lada haka hadisi ya tabbatar ko da ko a Makka take ko Madina ta yi a gida ya fi da ta je masallaci.

Ita kuma matar ko yarinyar dolene ta nemi izini kafin ta fita zuwa masallaci in ta je bada izinin uba ko miji ba ta saɓama  Annabi  (s.a.w) kuma ana ji mata tsoron fadawa cikin halaka na saɓama Manzon Allah (s.a.w) Kuma da mata za suyi sallarsu a gida yafi

lada da suje masallaci haka hadisai suka tabbatar mace ta yi sallah a gida ya fi da ta je masallaci.

Hadisi ya tabbata Ummu Humaidi ta zowajen Manzon Allah (s.a.w)  ta ce ‘’ Ina son in riƙayin sallah tare da kai a masallacin ka sai Manzon (s.a.w)  ya ce mata ‘’’ Nasan kina son kiyi sallah tare dani to amma kiyi sallarki adakin ki ya fi maki alheri da kiyi sallah a masallaci. (’’ Ahmad 6/371 da ibn Khuzaimah 3/95.

Gaskiyar labari dai shi ne mace ta yi sallarta agida ya fi lada da daraja da mutunci da ta je masallaci. ya kamata mata su gane cewa sallar su a uwar dakinsu ya fi lada da ta yi afalo, haka  hadisi ya nuna. Duba Attamhid na ibn AbdulBar 23/398 ya yi bayini sosai da ke nuna sallar mace adakinta ya fi lada da ta je masallaci.

 Mutane yanzu sun mai da addini yayi, ba shara’a ba ya dai kamata Malamai su nuna ma mata abin da ya ke daidai ba ya yi ba. A duba littafin Ahkamun Nisa’i na Amru bn Abdul Mun’in shafi na 20.)

Allah kasa mu gama lafiya.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments