Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Kallon Mace Yana Karya Azumi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan mutum ya yi dubi da-gangan ga mace ajnabiyyarsa (wacce babu haramcin aure a tsakaninsu), saboda kyanta, ko tufarta ko jikinta, - alhalin yana azumi- Shin azuminsa ya lalace ko kuma hakan makruhi ne; wato, shin Allah zai iya karbar azuminsa, sai kuma ya yi sakayya a gare shi a kan kallonsa? Ku yi mana fatawa a kan haka, da fatan Allah ya ba ku lada?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Haramun ne akansa ya kalli mata, idan kuma da sha'awa ne haramun din ta fi tsanani, saboda fadin Allah:

قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ۚ

MA'ANA: "Ka ce, Muminai su rintse sashen ganinsu, su kuma kiyaye farjojinsu", [Suratul Nur: 30].

Kuma saboda kasancewar sake ido yana daga cikin hanyoyin aukuwar alfasha, don haka, rintse ido wajibi ne, tare da kiyaye dukkan sabbuban aukuwar fitina, Sai dai kuma azuminsa ba zai lalace ba, matuƙar maniyyi bai fito masa ba.

Amma wanda ya yi maniyyi to, shi azuminsa ya ɓaci, kuma dole ya yi ramuko. Allah shi ne Majibincin dacewa!

MAJMU'U FATAWA WA MAƘAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 268-271).

ALLAH NE MAFI SANI.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments