Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayan Ta Haihu, Ta Yi Wajen Wata Biyu Jinin Al'ada Bai Dawo Ba

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu

Wata matace, ta haihu ne to ta yi wajan 2 month period nata baidawo ba sai randa aka dau azumi ta ga wani abu mai yauki kaman majina amman yana hadeda jini sai dai jini ba ja sosai bane kuma baya karni sanna kuma yayita zuwa ne kaman majina har tswon kwana uku to yanzu wannan kam za ta biya azumin ne sanna kuma intazo yin wanka wani irin niyya zatayi??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To wannan tambayar akwai wani abu a cikinta, abun kuwa shi ne akwai buƙatar musani shin sadda ta haihun ta ga jini kokuwa bata ganiba?? Idan ta ga jini sai jinin ya dauke shi ne bayan daukewarshin har watanni biyu bata ga al'adarta ba, sai bayan watanni biyun ta ga wannan kalarda tace tagani?? To idan haka take nufi, to inhar tana iya gane kalar jinin hailarta saita duba tagani, inhar wannan ruwan shi ne irin jinin hailarda tasaba gani dama aduk lokacin hailar, to shikenan wannan din datagani yanzu to hailace dan haka bayan sallah za ta rama azumin wayannan kwanakin sannan kuma niyyar wankan haila za ta yi.

Inkuwa sanda ta haihun kwata kwata bata ga jiniba sai wannan wanda tace taganshi a bayan watannin biyun to shima dai hukuncin iri dayane da bayaninda mukayi asama

Amma dan wannan ruwan bashi ne irin jinin hailarda tasabayi ba, to anan za ta bashi hukuncin damu fasadinne wato jinin ciwo, kenan azuminta na wayannan kwanakin sunyi, sannan kuma babu wankanda zatayi saidai wanka na tsafta da jin daɗi

Inkuma wannan kalar da ta gani ya zo matane kafin ta cika kwanaki 40 ko 60 da haihuwa shi ne ta ga wannan kalar ruwan to anan kuma jinin haihuwane dan haka ba ta da azumin wayannan kwanakin, sannan kuma wankan da zatayi shi ne na yankewar jinin haihuwa

Allah ya sa mudace

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments