Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Hukuncin Wanda yake gaggauta sahur da kuma yin buɗa baki cikin dare?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Wanda yake gaggauta sahur da kuma yin buɗa baki cikin dare?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wannan ya saɓawa shiriyar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kuma wannan koyine da yahudawa da kiristoci da kuma yan shi'a. Abinda yake Sunnah daga Manzon Allah shi ne gaggauta buɗa baki, kamar yadda ya zo ahadisin Sahal Manzon Allah ya ce "Mutane ba za su gushe cikin alkhairi ba matuƙar suna gaggauta buɗa baki". A hadisin Abu Huraira kuma yake cewa "Addini bazai gushe a bayyane ba matuƙar ana gaggauta buɗa baki, domin yahudawa da kiristoci sune suke jinkirta buɗa baki.

Shikuma suhur, abinda akeso shi ne a jinkirta shi har zuwa dab da ketowar alfijir, saboda hadisin Zaidu bin thabit Allah ya ƙara yarda dashi yake cewa "Mun yi suhur tareda Manzon Allah sai muka tashi mukaje mukayi sallah, sai Anas ya ce sai na tambayi Zaidu yaya gwargwadon gama suhur din da kiran sallah?? Sai ya ce gwargwadon mutum ya karanta ayoyi hamsin.

Dan haka yin ihtiyaɗi wurin barin suhur ya saɓawa Sunnah, ibnu Hajar Allah masa rahama yake cewa "yana daga cikin bidi'o'i munana da aka ƙirƙiro awannan zamanin shi ne ƙiran sallah na biyu kafin fitowar alfijir da kusan minti 15 a cikin watan Ramadan, gamida kashe fitilu wanda ake yinsu amatsayin alama na haramta ci da sha ga duk wanda zai yi azumi, azaton masu yin hakan shi ne sunayin ihtiyaɗi ne a cikin ibada, hakan ya sa kuma basa ƙiran sallah alokacin buɗa baki har sai rana da fadi da wasu mintuna duk wai dan su tabbatar da shigan lokaci azaton su, sai suka gaggauta suhur suka jinkirta buɗa baki, hakan ya haifar musu da Saɓawa sunnah, hakan ya sa alkhairi ya yi ƙaranci a cikin su, sharri ya yawaita musu, Allah ya mana taimako".

سسبعون مسألة مهمة في الصيام

WALLAHU A’ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments