Shin Ana Yin Zakkar Fidda-Kai Da Kuɗi, Kuma Wa Ya Kamata Na Ba?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, malam tambayata ita ce mutum zai iya ba wa ɗan'uwansa zakkar fidda-kai wadda suke uwa ɗaya uba ɗaya, sannan kuma don Allah a taimake mu a duba mana in mutum zai ba da Zakka fidda-kai na kuɗi nawa ne kowane mutum ɗaya zai bayar?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam, dama ita zakkar fidda-kai an shar'anta a ba wa talakawa ne, saboda haka matuqar wanda kuke uwa ɗaya uba ɗaya da shi ɗin nan yana daga cikin faqirai ko miskinai, to ya halasta ki ba shi zakkar fidda-kai, kawai sharaɗin dai ya zamana wanda za a ba zakkar yana daga cikin faqirai ko miskinai, kamar yadda malamai suka tabbatar ta la’akari da ayar Alqur’ani.

    Shi ko hukuncin yin zakkar fidd-akai da kuɗi, malaman Musulunci suna da fahimta guda biyu: na farko suna ganin ya halasta mutum ya yi zakkar fidda-kai da kuɗi, saboda su a fahimtarsu daga cikin manufar shar'anta zakkar fidda-kai shi ne don a faranta wa talakawa rai a ranar Eidi, saboda haka suke da fahimtar za a iya ba da kuɗin da zai yi daidai da qimar sa'i ɗaya na abinci, masu wannan fahimtar sun haɗa da: Imam Abu Haneefa, da Hasanul Basriy, da Umar ɗan Abdul'aziz, da Thauriy.

    Sai dai Is'haq da Abu Thaur sun ce qimar zakkar fidda-kai ba ya isarwa a yi da kuɗi har sai in akwai lallura. Amma fahimtar mafi yawan malaman Musulunci ita ce: Qimar Zakkar fidda-kai da kuɗi ba ya isarwa kamar yadda Imam Malik, da Imam Ahmad, da Ibn Munzhir suka faɗa. Duba ALMAJMU'U 6/144 na Imamun Nawawiy.

    Saboda haka, abin da ya fi cancanta shi ne a fitar da zakkar fidda-kai da nau'in abincin da aka fi ci a garin da mutum yake, sai idan akwai lallura ne sannan a ba da kuɗin da ya yi daidai da qimar sá'i ɗaya na abinci.

    Sai dai fa ni ban san ko nawane qimar kuɗin zakkar fidda-kai a kuɗin qasarmu ba, saboda ni da abinci nake yi ba da qima na kuɗi ba, abin dai da ya wajaba a kiyaye shi ne: Asali dai kowane mutum ɗaya da zai yi fidda-kai zai ba da abinci ne SÁ'I ɗaya, sá'i ɗaya kuma shi ne Muddun Nabiyyi huɗu.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga masu buqatar shiga Wannan Group zasu iya bi ta links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.