𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam don Allah ina son karin bayani ne
a kan zakkar fidda-kai?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, Zakatul Fiɗri ita ce zakkar
fidda-kai da Hausa, wato sadaka ce da take zama wajibi ta dalilin kammala
azumin Ramadana, domin tsarkake mai azumi daga wasu ƴan
kurakurai da ya yi a lokacin azuminsa.
Gwargwadon Abin Da Ake Fitarwa Na Zakkar Fidda-Kai:
Zakkar fidda-kai ana fitar wa da kowane mutum ɗaya awo ne na sá'i
ɗaya, idan ba a
sami ma'aunin sá'i ba, to sai a auni Muddun Nabiyyi huɗu, dai-dai yake da
sá'i ɗaya. Idan mutum
bai fahimta ba, ko ba a sami ma'aunin Muddun Nabiyyin ba, to ya haɗa tafukan
hannayensa biyu a haɗe, sai ya kamfato hatsin sau huɗu cikin hannayen
nan nasa a haɗe, wannan shi ne sá'in Annabi s.a.w. kuma shi ne awon
muddun Nabiyyi huɗun can kamar yadda Allama Ibn Baaz ya bayyana.
Duba Fataáwá Nurun Alad-Darb (15/277).
Hukuncin Zakkar Fidda-kai:
Zakkar Fidda-kai wajibi ne a kan kowane Musulmi, saboda
hadisin da Abdullahi ɗan Umar Allah ya qara masa yarda ya ruwaito cewa:
"Annabi s.a.w. ya farlanta zakkar fidda-kai a watan
Ramadana, sá'i ɗaya na dabino, ko sá'i ɗaya na alkama a
kan bawa da ɗa, da namiji, da tamace, da yaro da babba daga cikin
Musulmai".
Bukhariy (1503), Muslim (984).
Kuma mafi yawan malaman Musulunci sun haɗu a kan cewa
zakkar fidda-kai farilla ce, kamar yadda Imam Ibn Munzhir ya bayyana.
Al'ijmá'u (47).
Ya wajaba mutum ya fitar wa da kansa zakkar fidda-kai, da duk wanda suke ciyar da su ya lizimce shi,
waɗanda suka haɗa da matarsa da makusantansa, haka nan zai fitar wa da
bawansa.
Sannan ɗan da ke ciki, wanda ya isa a hura masa rai (wato wanda
ya kai wata huɗu), za a iya fitar masa da zakkar fidda-kai, amma ba waji
ba ne, saboda an sami hakan daga wasu magabata.
Zakkar Fidda-Kai Ba Ta Wajaba Sai Da Sharuɗɗa Guda Biyu:
1. Dole sai mutum ya zama Musulmi, wato ba ta wajaba a
kan wanda ba musulmi ba.
2. Kuma ya zama abincin mutum da iyalansa ya yi rara,
wato sun wadata da abinci a ranar Eidi har suna da raguwar wanda za su ba da
sadaka da shi.
Dubi Alfiqhul Muyassar Fiy Dhau'il Kitábi Was Sunnah
(141), na Majmú'atun Minal Mu'allifeen.
Lokacin Da Ake Fitar Da Zakkar Fidda-Kai:
Zakkar Fidda-kai tana zama wajiba a fitar da ita ce bayan
faɗuwar Rana ta yinin
qarshe na Ramadan, misali idan yau ne ake sa ran za a kammala azumi, to da
zarar Rana ta faɗi, lokacin wajabcin ba da zakkar fidda-kai ya shiga ke
nan. Har zuwa kusa da kafin lokacin sallar Eidi.
Abdullahi ɗan Abbas ya ruwaito cewa: Annabi s.a.w ya ce: "Duk
wanda ya ba da zakkar fidda-kai kafin sallar Eidi, to zakka ce karɓaɓɓiya, wanda kuma ya
ba da ita bayan idar da sallar Eidi, to sadaqa ce daga cikin sadaqoqi".
Abu Dáwud (1609), Ibn Majah (1827).
Kuma ya halast mutum ya ba da zakkar tasa kwana ɗaya ko biyu kafin
ranar Eidi, kamar yadda aka ruwaito cewa Abdullahi ɗan Umar yakan yi.
Duba Almugniy (3/90) don qarin bayani.
Hikimar Shar'anta Zakkar Fidda-Kai:
Hikimar da ke cikin Shar'anta zakkar fidda-kai ita ce;
don a sauqaqa wa talakawa ta hanyar wadatar da su ga barin roqo a ranar Eidi,
da sanya masu farin ciki a ranar farin cikin Musulmai saboda zuwan Ranar Eidi,
da kuma tsarkake wanda zakkar ta wajaba a gare shi bayan kammala azumin
Ramadana daga yasasshen magana da kalaman batsa.
Sahihu Fiqhus Sunnah (2/79), na Abu Malik.
Allah ne masani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga masu buqatar shiga Wannan Group zasu iya bi ta links ɗin mu...
HUKUNCIN ZAKKAR
FIDDA-KAI
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam don Allah ina son karin bayani ne a
kan zakkar fidda-kai?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, Zakatul Fiɗri ita ce zakkar fidda-kai da Hausa, wato
sadaka ce da take zama wajibi ta dalilin kammala azumin Ramadana, domin
tsarkake mai azumi daga wasu ƴan kurakurai da ya yi a lokacin azuminsa.
GWARGWADON ABIN DA
AKE FITARWA NA ZAKKAR FIDDA-KAI
Zakkar fidda-kai ana fitar wa da kowane mutum ɗaya awo ne na sá'i ɗaya, idan ba a sami
ma'aunin sá'i ba, to sai a auni Muddun Nabiyyi huɗu,
dai-dai yake da sá'i ɗaya.
Idan mutum bai fahimta ba, ko ba a sami ma'aunin Muddun Nabiyyin ba, to ya haɗa tafukan hannayensa biyu a
haɗe, sai ya kamfato
hatsin sau huɗu cikin
hannayen nan nasa a haɗe,
wannan shi ne sá'in Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) kuma shi ne awon muddun
Nabiyyi huɗun can
kamar yadda Allama Ibn Baaz ya bayyana.
Duba Fataáwá Nurun Alad-Darb (15/277).
HUKUNCIN ZAKKAR
FIDDA-KAI
Zakkar Fidda-kai wajibi ne a kan kowane Musulmi, saboda
hadisin da Abdullahi ɗan
Umar Allah ya qara masa yarda ya ruwaito cewa: "Annabi (Sallallahu alaihi
Wasallam) ya farlanta zakkar fidda-kai a watan Ramadana, sá'i ɗaya na dabino, ko sá'i ɗaya na alkama a kan bawa da
ɗa, da namiji, da
tamace, da yaro da babba daga cikin Musulmai".
Bukhariy (1503), Muslim (984).
Kuma mafi yawan malaman Musulunci sun haɗu a kan cewa zakkar
fidda-kai farilla ce, kamar yadda Imam Ibn Munzhir ya bayyana.
Al'ijmá'u (47).
Ya wajaba mutum ya fitar wa da kansa zakkar fidda-kai, da
duk wanda suke ciyar da su ya lizimce shi, waɗanda
suka haɗa da matarsa
da makusantansa, haka nan zai fitar wa da bawansa.
Sannan ɗan
da ke ciki, wanda ya isa a hura masa rai (wato wanda ya kai wata huɗu), za a iya fitar masa da
zakkar fidda-kai, amma ba wajibi ba ne, saboda an sami hakan daga wasu
magabata.
ZAKKAR FIDDA-KAI BA
TA WAJABA SAI DA SHARUƊƊA GUDA BIYU
1. Dole sai mutum ya zama Musulmi, wato ba ta wajaba a kan
wanda ba musulmi ba.
2. Kuma ya zama abincin mutum da iyalansa ya yi rara, wato
sun wadata da abinci a ranar Eidi har suna da raguwar wanda za su ba da sadaka
da shi.
Dubi Alfiqhul Muyassar Fiy Dhau'il Kitábi Was Sunnah (141),
na Majmú'atun Minal Mu'allifeen.
LOKACIN DA AKE FITAR
DA ZAKKAR FIDDA-KAI
Zakkar Fidda-kai tana zama wajiba a fitar da ita ce bayan faɗuwar Rana ta yinin qarshe
na Ramadan, misali idan yau ne ake sa ran za a kammala azumi, to da zarar Rana
ta faɗi, lokacin
wajabcin ba da zakkar fidda-kai ya shiga kenan. Har zuwa kusa da kafin lokacin
sallar Eidi.
Abdullahi ɗan
Abbas ya ruwaito cewa: Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Duk
wanda ya ba da zakkar fidda-kai kafin sallar Eidi, to zakka ce karɓaɓɓiya, wanda kuma ya ba da ita bayan idar da
sallar Eidi, to sadaqa ce daga cikin sadaqoqi".
Abu Dáwud (1609), Ibn Majah (1827).
Kuma ya halast mutum ya ba da zakkar tasa kwana ɗaya ko biyu kafin ranar
Eidi, kamar yadda aka ruwaito cewa Abdullahi ɗan
Umar yakan yi.
Duba Almugniy (3/90) don qarin bayani.
HIKIMAR SHAR'ANTA
ZAKKAR FIDDA-KAI
Hikimar da ke cikin Shar'anta zakkar fidda-kai ita ce; don a
sauqaqa wa talakawa ta hanyar wadatar da su ga barin roqo a ranar Eidi, da
sanya masu farin ciki a ranar farin cikin Musulmai saboda zuwan Ranar Eidi, da
kuma tsarkake wanda zakkar ta wajaba a gare shi bayan kammala azumin Ramadana
daga yasasshen magana da kalaman batsa.
Sahihu Fiqhus Sunnah (2/79), na Abu Malik.
Allah ne masani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.