Neman Yafiyar Babba-Da-Jaka

    Balbela ta tuntsire da dariya, ta taɓa fikafiken Kurciya, ta ce: "Ƙawata kin ji abin da Babba-da-jaka ya ce ran nan?

    Kurciya ta ce: "Kin san ni yanzu ba damuwa na yi da harkokinsa ba, sukuwa ta ƙare saura zamiya, Babba-da-jaka dai lokaci ya yi... Yauwa! Wai me ya ce ne?

    "Cewa ya yi wai yana neman yafiyar tsuntsayen dajin nan, gaba É—aya!" Balbela ta amsa.

    "Zancen wofi ke nan! Lokacin da suke gallaza mana, muna neman su sassauta mana, ba izgili su kai tai mana ba?

    Su kai ta faɗa mana baƙaƙen maganganu, suna cewa ba mu da haƙuri, mu ɗin ragwaye ne dai sauransu? Don haka ni ma tun da ba su ji ƙyan mu ba lokaci da muke buƙata, to su je, mun bar su da fitowar rana da faɗuwarta."

    Hazbiya da ke gefe ta tsalma baki, ta ce: "Duk abin da aka shuka shi za a girba, Babba-da-jaka dai ya yi surfa mu son ransa, yanzu Tsuntsayen da akai ta kashewa a mulkinsa sakamakon sakaci da lalacinsa, duniya za su dawo su yafe masa?

    Yanzu tsuntsayen da ba a haifa ba, in suka zo duniya suka tarar da irin É“arnar Babba-da-jaka, ya tafka, ta ya za su yafe masa?"

    Tattabara ta ce: "Ai maganar yafiya ma ba ta taso ba, in har ana cewa an yafe, to haka za sui ta zaluntar mutane suna cewa a yafe musu, don haka ni dai da dukkanin jinsin Tattabarai dajin nan ba mu yafe ba, a faÉ—a wa Babba-Da-Jaka mu haÉ—u ranar sakamako!"

    Da ya ke dare ya fara yi, tsuntsaye kowa ya nufi sheƙarsa don shimfiɗa fiffikensa.

    Daga

    Mukhtar Sipikin

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.