𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mutumin da ya yi bacci
tsawon wuni gaba ɗaya tun bayan asuba har faɗuwar rana, shin
azuminsa ya yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Shaikh Ahmad Annajmi Allah ya masa rahama yake cewa
"Akwai banbanci tsakanin bacci mai nauyi da mara nauyi, da kuma tsakanin
suma mai tsawo da mara tsawo, dan haka bacci komin nauyinsa ko tsawonsa mai shi
yana nan a mukallafi, Shari'a bata faɗi akansa ba, sai dai za a jinkirta masa zuwa lokacin da
zai farka, idan shi ya sabbabawa
kansa baccin to yanada zunubi (kamar yasha ƙwaya dan ya
wuni bacci) idan kuma bashi ya sabbabawa
kansa ba to babu komai akansa kawai zai tashi ya rama abin da ake binsa na
salloli kuma azuminsa yayi, saɓanin wanda kuma ya haɗu da hatsari ƙwaƙwalwarsa ta bugu ya suma tsawon lokaci
to shi ana ɗauke masa Shari'a kamar mahaukaci, wannan shi ne abin da ya bayyana mini awannan mas'alar,
amma idan suman bai yi tsayiba to yanada hukuncin bacci".
WALLAHU A'ALAM
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.