𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mutum ne ya fara azumi a wani gari/ƙasa sai ya yi tafiya zuwa wata ƙasa don ya ƙarasa azuminsa a can, sai ya kasance ƙasar da ya fara azumi a ciki sun riga fara ɗaukan azumi, to yaya zai yi??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Shaikh Ahmad bin Yahya Annajmi Allah ya masa rahama yake
cewa "Yana wajaba akansa da ya gina azuminsa akan lissafin garin da ya
koma, sawa'un sun riga fara dauka ko ba su riga ba, sai dai kawai idan ya
kasance garin da ya fara azumi sun riga wancan garin da ya koma ɗaukan azumi kuma
ya kasance ba su ga wata ba za su cika azumi talatin to shi bazai cika tare da
su ba (domin idan ya cika da su zai zama
ya yi azumi talatin da ɗaya kenan) zai ajiye azumi amma aɓoye bazai yi bazai
bayyana ba, Allah ya sa mu dace".
سبعون مسألة مهمة في الصيام
WALLAHU A'ALAM
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.