Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan mace ta yi tsarki da rana a watan Ramadan, ko matafiyi ya dawo gida da rana a watan Ramadan, shin yana wajaba a kansu su kame bakinsu?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan mace ta yi tsarki da rana a watan Ramadan, ko matafiyi ya dawo gida da rana a watan Ramadan, shin yana wajaba a kansu su kame bakinsu??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Shaikh Ibnu baaz Allah ya masa rahama yana cewa "yana wajaba a kansu su kame bakinsu, wannan shi ne zance mafi inganci cikin zantukan malamai, domin uzurin da ya ba su damar ajiye azumin ya kauce, kuma za su rama azumin wannan yinin. Haka da ace bayyanar watan Ramadan zaizowa Musulmai da rana da ya wajaba musu su kame bakunansu, sannan kuma su rama azumin wannan ranan kamar yadda jumhurin malamai suka tafi akai, haka shima matafiyi idan ya dawo da rana zai kame bakinsa saboda gushewar hukuncin tafiya akansa kuma zai rama azumin wannan ranan".

سبعون مسألة مهمة في الصيا.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments