Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Hukuncin Bayyana Karatu A Sallar Nafila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Nafilar Bayan Sallar Magariba Bayyana Karatu Ake, Domin Naga Wadansu Suna Bayyana Karatu Wadansu Kuma Sunayi A Aboye Wanne ya fi Inganci A cikinsu.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Abunda yake asali shi ne bayyana karatu a sallolin nafilfilin da ake yinsu daddare, da kuma ɓoye karatu a cikin wadanda ake yinsu da rana.

Imamun Nawawy Rahimahullah ya ce: sallar idi da ta rokon ruwa da sallar tarawihi da sallar kisfewar wata sunnah ne bayyana karatu a cikinsu babu saɓani.

Nafilfilin rana sunnah shi ne ɓoye karatu a cikinsu babu saɓani.

Nafilolin dare wanda ba sallar tarawihi ba ana bayyana karatu a cikinsu, Alƙazy da mai littafin attahzeeb ya ce: Mutum zaiyi tsaka tsakiya a cikinsu wataran ya ɓoye karatun wataran kuma ya bayyana.

Amma sunnoni jerarru da'ake yinsu bayan sallolin farillah ko kafinsu a mazhabarmu shi ne dukkansu za a ɓoye karatunsu ne.

Alƙazi ya nakalto a cikin sharhi muslim daka wasu cikin salaf cewa ana bayyana karatun nafilar sallar asubah raka'atanul fajar kenan, daka jamhur ɗin malamai shi ne ɓoye karatunsu kamar mazhabarmu. sai imamun nawawi ya ambaci hadisan dasukazo a kan haka Almajmu'u (3/357).

Yazo a cikin kasshaful ƙina'a (1/441) Makaruhi ne mai sallah ya bayyana karatu a cikin nafilar rana in ba asallar kisfewar rana ba kota rokon ruwa ba, a cikin sallar nafilar dare kuma ya kiyaye wanda suke tare dashi ko yake kusa dashi, ko wanda zai cutu da bayyana karatunsa sai ya ɓoye, idan kuma akwai wanda zai amfana da bayyanawarsa sai ya bayyana.

Rana ana nufin daka hudowar rana ba daka hudowar alfijir ba, dare ana nufin daka faduwarta harzuwa sake hudowarta.

Babu saɓani sunnah shi ne ɓoye karatu asallolin rana, Idan mai sallah ya bayyana karatu a sallar rana saboda hakan zaifi sashi tsoran Allah da kuma tunatar dashi, babu laifi akansa, tare dacewa sunnah dakuma abunda ya fi shi ne ɓoyewa.

Shaik bin baz Rahimahullah ya ce: " Idan mutum yana sallah shi kaɗai an shar'anta masa ya yi abunda ya fi masa ransa na bayyana karatu ko ɓoyewa cikin  dare idan  asallar nafila ne, idan  bayyana karatunsa bazai cutar da kowa ba, idan akwai wani akusa dashi wanda zai cutu da bayyanawar ko mai bacci ko wasu masu sallar daban ko masu karatu an shar'anta masa ɓoye da sautinsa.

Amma sallar nafilar rana kamar sallar duha,  da nafilolin da'ake akowacce sallah da sallar azahar da la'asar sunnah shi ne ɓoye karatu.

Ya halatta wani lokacin liman ya bayyana wasu ayoyi a sallar azahar da la'asar saboda hadisin Abu Ƙatada ya ce manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam ya kasance yana jiyar damu wasu ayoyi asallar azahar da la'asar.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments